Rundunar soji ta musamman, Operation Safe Haven (OPSH) da ke wanzar da zaman lafiya Jihar Filato, ta ce ta kwato haramtattun muggan makamai guda 130 a jihar da sauran yankunan da ta gudanar da aikin hadin gwiwa.
Maj.-Gen. Abdusalam Abubakar, Kwamandan Operation ne ya bayyana haka a lokacin da yake mika makaman da aka kwato ga Cibiyar Kula da Kananan Makamai ta Kasa (NCCSALW) ranar Litinin a Jos.
- An Ƙaddamar Da Shirin Yaƙi Da Rikicin Ƙabilanci A Jihar Filato
- Tinubu Ya Bada Umarnin Binciko Wadanda Suke Kashe-Kashe A Filato
Abubakar, ya jaddada kudirinsa na ganin an dakile matsalar rashin tsaro a jihar Filato, ya ce an yi amfani da hanyoyin dabaru wajen kwato makaman.
“Rundunar sojojinmu sun jajirce wajen duba duk wani nau’in laifuka da tarzoma; Dakarun sun kuma ci gaba da kai farmaki, inda suka gudanar da ayyukan kwato manyan makaman haramtattu.
“Sojojin OPSH sun Samu nasarar wato kananan makamai 130 daga masu aikata laifuka.
“Za mu ci gaba da yin aiki tare domin dakile ayyukan masu aikata laifuka a yankin mu na hadin gwiwa.
“Wannan shi ne karo na biyu da OPSH ke mika mana muggan makamai da aka kwato, muna yaba musu kan wannan kokarin.
“Don haka muna kira ga jama’a da su tallafa wa sojoji da sauran jami’an tsaro ta hanyar bayar da bayanai da tattara bayanan sirri don kawo karshen duk wani nau’in rashin tsaro a kasarmu,” cewarsa.