Solkjaer Ya Yi Magana Da Dan Wasa Halland

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun ruwaito cewa kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunner Solkjaer, ya tattauna da dan wasan gaba na kungiyar RB Red Bull Salzburg, Erlin Halland, wanda kungiyoyi da dama suke zawarci.

Duk da cewa dan wasan gaban dan asalin kasar Norway ya kasa taimakawa kungiyarsa ta samu zuwa zagaye na biyu na gasar cin kofin zakarun turai amma kokarin da yayi yasa manyan kungiyoyi sun fara zawarcinsa.

A kwanakin baya dai dan wasan, mai shekara 19 a duniya ya bayyana cewa yana fatan kammala kakar wasa a kungiyarsa da yake a yanzu amma yadda manyan kungiyoyi suke kokarin daukar sa yasa yanzu ya fara canja shawara.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United dai tana daya daga cikin kungiyoyin da suke zawarcin matashin dan wasan kuma a ranar Juma’a aka bayyana cewa kociyan kungiyar yaje har kasar Austria yayi Magana da dan wasan akan komawa Manchester United.

Ba wannan ne karo na farko ba da Solkjaer da dan wasan suka hadu domin kociyan na Manchester United shine ya fara saka dan wasan a babbar kungiya a lokacin da Solkjaer yake koyar da kungiyar Molde ta kasar Norway shima Haaland yana kungiyar a matsayin matashi.

Kungiyoyin Jubentus da Dortmund da RB Lipzeig ta kasar Jamus duka suna zawarcin matashin dan wasan inda tuni akace dan wasan ya tattauna da Borussia Dortmund da RB Lipzeig din akan kamawa daya daga cikinsu a watan Janairu.

Exit mobile version