Abba Ibrahim Wada" />

Soyayya Ce Ta Sa Na Koma Real Madrid -Zidane

Zinaden Zidane ya sake karbar ragamar horar da Real Madrid a ranar Litinin watanni 9 bayan ajiye aikin horar da kungiyar bisa radin kansa, lokacin da ya jagoranceta lashe kofin gasar zakarun Turai sau 3 a jere.
Komawae ta Zidane ta biyo bayan sallamar kocinta Santiago Solari da kungiyar Madrid din ta yi, inda ta sake kulla yarjejeniyar shekaru uku da Zidane, da za ta kare a ranar 30 ga watan Yuni, na shekarar 2022.
Zidane ya koma Real Madrid a daidai lokacin da ya rage wasanni 11 kawai a kammala gasar La Liga ta bana, wadda kungiyar ke matakin ta uku da maki 51, tazarar maki 12 tsakaninta da babbar abokiyar hamayya Barcelona da ke jagorantar La Ligar da maki 63.
Matakin na Zidane dai ya zowa da dama a ba zata, la’akari da cewa a waccan lokacin da ya ajiye aikinsa, ya bar kungiyar ne a matsayi mai kyau, cike da samun nasarori, amma a yanzu ya karbe ta tana cikin halin kaka nika yi.
Sai dai yayin zantawa da manema labarai, Zidane ya ce ya yanke shawarar komawa Madrid saboda kaunar kungiyar da yake da kishinta, dan haka a lokacin da shugabanta Florentino Perez ya tuntube shi, sai ya kasa kin amsa bukatar.
Tun a lokacin da Barcelona ta lallasa Real Madrid a jere a gasar la Liga da ta Copa del Rey aka sa ran za ta kori kocinta Madrid a wannan lokaci wato Santiago Solari, amma sai aka jinkirta, daga bisani kuma Ajad ta fitar da ita daga gasar zakarun Turai, lamarin ya sa ta tabbata Real Madrid ta yi barin Kofuna uku cikin mako daya.

Exit mobile version