Gwamnatin tarayya ta fara kwashe daliban Nijeriya da ke Kasar Sudan ta hanyar motocin safa na alfarma zuwa Kasar Masar.
Abike Dabiri-Erewa, shugabar hukumar ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje (NIDCOM) ta yada hotunan daliban a Kasar Sudan suna cikin jerin gwanon motocin bas zuwa Kasar Masar, wanda daga nan za su nufi Nijeriya.
- EFCC Ta Gurfanar Da Kakakin Jihar Ondo A Gaban Kotu
- Allah Ya Yi Wa Magatakardan Jami’ar Bayero, Jamil Ahmad Salim Rasuwa
Hukumar ta ce tawagar daliban Nijeriya da ke Sudan sun karbi wasu motocin bas a jiya don jigilar daliban zuwa kan iyakokin da ke kusa da Masar.
Daliban za su tashi ne a yau sannan daga bisani a dauke su daga Kasar Masar sannan su zarce zuwa Nijeriya.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa wasu motocin bas guda biyar masu daukar kujeru 200 ne aka ce sun shiga dandalin taro na Jami’ar International University Of Africa da ke Khartoum da misalin karfe 7:30 na yamma agogon kasar (5:30pm – agogon Najeriya), tare da jami’an tsaro a mota kirar Hilux guda biyu.
A baya dai Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Mustapha Habib Ahmed ya gana da Jakadan Nijeriya a Masar, Ambasada Nura Rimi, akan shirye-shiryen karbar ‘yan Nijeriya daga Sudan zuwa Masar.