Sudan Za Ta Mika Wa Kotun Duniya Omar Albashir

Gwamnatin Kasar Sudan ta ce za ta mika tsohon shugaban kasar Omar Albashir ga kotun duniya wato ‘International Criminal Court’.

Ministan harkokin wajen kasar Maryam al-Mahdi, wanda ta tabbatar da hakan ranar Laraba, ya kara da cewa za a gurfanar da hambararren shugaban kasar ne tare da jami’an gwamnatinsa bisa rikicin da ya faru a yankin Darfur.

Albashir ya kwashe fiye da shekara 30 yana mulkin kasar amma aka hambarar da shi a shekarar 2019, yana fuskantar zargin laifukan yaki da na cin zarafin bil adama sakamakon rikicin Darfur.

Exit mobile version