Wata matar aure mai kimanin shekara 20, mai suna Caroline Barka, ta caka wa mijinta wuka mai shekara 38 mai suna Barka Dauda, Caroline Barka, tana zaune a Ungwar Tamiya, da ke karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa, matar ta yi wannan danyen aikin ne lokacin da suka harke da fada sakamakon wata sa-in-sa a tsakaninsu.
Wannan sa-in-sa ta yi nisa a tsakaninsu, ana cikin haka sai ya dawo gida a guje, ya zo ya dauko giya, ya sha ya yi tatul, yana tangadi har ya fada kan wata yarinya karama.
Da ma dai Angered yana shan giya, bayan ya dawo gida ba tare da ya shigo da wani abu ba a matsayinsa na mai gida, sai fada ya kaure tsakaninsu, a cikin fadan ne matar ta raruno wuka, ta daba wa mijin nata, kamar yadda wani dan cikin gida ya bayar da labari.
Ganin haka, nan da nan aka dauki mutumin zuwa asibiti wanda kuma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Rundunar ‘yansandan jihar Adamawa, wadda ita ta fara gano wannan lamari, ta ce, ranar Juma’a 20 ga watan Yuli, ta kama wadda ake zagin da kashe mijin nata.
“’Yansanda sun kama wadda ake zargin a karamar hukumar Madagali sakamakon wani rahoton sirri da suka samu.
“Zuwa yanzu, bincike ya tabbatar da cewa, wannan mata tana goyo ne, kuma tana da ‘ya’ya da wannan miji nata da ta kashe,”.
An samu wannan rahoto ne a cikin wata sanarwa da daga jami’in ‘yansanda SP Suleiman Nguroje.