Bari mu fara da wasu tambayoyi da aka dade ana yi. – Ina Data din da muke saya a Kamfanonin MTN/Airtel Glo, 9 Mobile suke tafiya? – Ta yaya Facebook da WhatsApp da sauran Social Media Platforms suke samun kudi? – A ina manyan kamfanonin yanar Gizo suke samun kudi? Menene ribar kamfanonin sadarwa?
Wadannan ba sababbin tambayoyi ba ne amma suna yawan shige wa mutane duhu, musamman a wannan lokacin da al’amuransu suke sake ruruwa a kullum a duniya.
- Kasar Sin Ta Mika Wasu Takardun Amincewa Da Yarjejeniyoyi Biyu Ga ILO
- Yadda ‘Yan Bindiga Suka Hallaka Ma’aikata Hudu Da ‘Yansanda Biyu A Kamfanin Sarrafa Tasa
A mafi yawan lokuta ana kuskuren fahimtar yadda al’amuran yanar gizo da sadarwa suke, musamman ma idan ka dauki tambaya ta farko da ke sama ko kuma ta biyu.
Idan muka dauki tambaya ta farko. Ina Data din da muke saya a kamfanonin MTN, Airtel Glo, da 9 Mobile suke tafiya?
To Data din da muke saya a kamfanonin MTN, Airtel ko Glo da sauransu ba ta da bambanci da fetir din da ake sa wa mota ko inji; duk daga karshe iska yake bi, to ita ma data din haka ne.
Idan ka sayi fetir ka zuba a inji kuma ka tayar, ka yi amfani da shi, daga karshe idan ka bude tankin za ka ga babu komai, to haka Data din waya yake.
Kawai ana sayarwa ne saboda hanyar samun kudi, kamar dai yadda ake sayar da fetir don samun kudi.
Don haka, a iska yake tafiya kai kadai kake amfanarta kamar dai fetir din injinka ko mota.
Ta Yaya Facebook da WhatsApp da Sauran Social Media Platforms Suke Samun Kudi? Kamfanonin Facebook, WhatsApp, Telegram, Google, Instagram da sauransu suna samun kudi ne ta hanyoyi da dama. Mafi yawan hanyoyin a bayyane suke wato tallace-tallace.
Facebook, Instagram, Twitter, LinkedIn, TikTok da sauransu suna samun kudi ta hanyar tallace-tallace wato adbertisements.
WhatsApp ba ya saka talla, amma yana samun kudi ta hanyar ‘yan kasuwa ko debelopers din da suke subscription na seta automatic messages dinsa.
Telegram ba ya saka talla, yana samun kudi ta hanyar bot din da mutane suke subscription wajen saitawa kusan irin na WhatsApp.
Wikipedia ba ya talla, babbar hanyar samun kudinsa shi ne donation, wato mutane da kamfanoni suna zuba musu abin da suka samu don nuna jindadinsu, Google yana daga cikin manyan donors dinshi.
Google yana talla ta hanyoyi da dama, kamar Google AdWords ko AdSense ko SEM da sauran hanyoyinsu na subscriptions.
YouTube yana talla ta hanyar Google AdSense saboda a karkashin kamfanin Google yake. Wasu suna tunanin Data din mutane YouTube yake sarrafawa ya samu kudi, a’a ba haka batun yake ba. —Yahoo yana talla, shi ma yana amfani da Google AdSense.
Paystack, PayPal, Flutterwabe da sauransu ba sa talla, suna samun kudi ne ta hanyar cajarka idan ka yi transaction.
A takaice, babu wani kamfani da ke zuke maka Data din da kake saya a kamfanin kamfanonin sadarwar nan.
Data dinka tana karewa ne kawai saboda ka sake saya, kamar dai yadda na bayar da misali da fetir.
A Ina Manyan Kamfanonin Yanar Gizo Suke Samun Kudi?
To kamar dai abin da na rubuta a sama, haka yake.
A yanzu shafukan yanar gizo suna samun kudi ne ta hanyoyi da dama, amma dai tun daga manyan shafukan har kanana yawanci tallace-tallace ne.
Hanya ta biyu kuma suna amfani da subscriptions din users dinsu ne, wato kamar yadda muke subscription na sayen ‘domain name’ da sauransu, ko kuma subscription na upgrading din account kamar yadda LinkedIn yake yi.
Hanya ta uku wasu kuma suna sayar da kayayyakinsu, kamar Amazon, sannan su ma suna karban transaction charges kamar yadda ake yi a Stackplaza, da Jumia da sauransu.
Sannan kamar Wikipedia shi ma hanya ta biyunsa shi ne sayar da T-Shirt mai tambarinsa wanda mabiyansa suke saya.
Hanya ta hudu kuma wasu suna harkar bayan fage, wato akwai abubuwan da ba su dace ba wanda gwamnati take sa ido a kai kamar sayar da bayanan mutane da sauransu.
Menene Ribar Kamfanonin Sadarwa? To ribar kamfanonin sadarwa irin su MTN da Airtel sayar da katin kira da Data din browsing da suke yi, haka nan sayar da layuka da sauran serbices dinsu.
Ko a yanzu Data bendors ba karamin kudi suke samu ba, to ballantana shi kuma kamfanin.
Idan ka sayi katin kira ya tafi a iska, haka ma Data dinka ta tafi a iska. Lokacin da ake 2go an dauka Data suke sarrafa wa, a’a ta hanyar ‘Go credits’ din da muke saya ne mu yi chatting rooms.