Wakilin kasa a hukumar lafiya ta duniya, Walter Mulombo, ya ce sama da ‘yan Nijeriya 30,000 ne ke mutuwa sakamakon cututtuka masu alaka da shan tabar sigari a duk shekara.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja a yayin kaddamar da wani shiri mai taken Kula da kiwon lafiya ta hanyar kula da shan Tabar Sigari da kungiyar Development Gateway (IREX) tare da hadin gwiwar ma’aikatar lafiya ta Shirya, don gudanar da bukukuwan ranar yaki da shan tabar Sigari ta duniya ta bana.
Ya ce adadin ya zarce na wadanda suka mutu daga cutar COVID-29 wacce ta kashe mutane 3,144 a kasar ya zuwa yanzu.
Ya bayyana cewa, illar shan taba kamar Bam ne da ake bashi lokacin fashewa.
Karamin ministan lafiya, Adeleke Mamora, ya ja kunnen ‘yan Nijeriya da su guji shan tabar sigari.