Ginin bene mai hawa uku ya rushe a sanannen titin Bende dake tsohon garin fatakwal, Jihar Rivers.
A cewar shaidun gani da ido, ginin, wanda aka gina shi shekaru da dama da suka gabata, ya ruguje ne da misalin karfe biyu na daren Laraba.
“Ginin ya kasance daya daga cikin gine-gine mafi tsufa a garin tsawon lokaci tin zamani mulkin mallaka, wanda ana zaton yana daga cikin kadarorin da aka bari a garin fatakwal bayan yakin basasa.
“Ginin ya rushe ne da misalin karfe biyun dare na ranar Laraba amma kawo yanzu babu sanarwa dake nuna an rasa rai yayin faruwar lamarin, sakamokon tsawon lokaci da ginin ya dauka babu kowa aciki”
Lokacin da aka tuntubi Jami’an hukumar ‘Yan Sanda na sashen hulda da jama’a na Jihar Rivers, Iringe Grace Koko, ya ce babu wani mai zama a ginin kafin ya rushe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp