Babban ma’aunin da za a gane bunkasuwa ko karfin tattalin arzikin kasa shi ne ko wane iyali ya wadatu da ababen more jin dadin rayuwa. Ta wannan gabar ce za mu fahimci yadda kasar Sin ta yi fice ta fannin bunkasuwar tattalin arziki tsakaninta da sauran kasashen duniya. Hasali ma dai Sin ta dade da cimma wannan matsayi na kasa mai ingantaccen bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri. Wannan yana daya daga cikin manyan dalilan da suka karawa jama’a kwarin gwiwa kan tattalin arzikin kasar Sin.
Sin ta samu cimma wannan matsayi sakamakon kyakkyawan shugabanci, hangen nesa da kuma bude kofa ga duk wanda yake sha’awar zuba jari ba tare da la’akari da kasar da ya fito ba.
- Peter Obi Ya Ziyarci Bauchi, Ya Gana da Gwamna Bala Mohammed
- Majalisar Dattawa Ta Buƙaci A Kafa Sansanin Soji a Jihar Binuwai
Jerin masana’antu, kama daga na kera kayan lantarki, kayan gine-gine, sufuri ya zuwa masana’antun saka tufafi, sun sanya Sin ta yi zarra a duniya, inda ta kasance kasar da ta fi kowace kasa fitar da kayayyakinta zuwa kasuwannin duniya.
Domin kuwa a wannan zamani, zai kasance abu mai wuya ka samu gidan da ba a amfani da kayayyakin da aka kera daga Sin. Ba wai a kasashe masu tasowa ba, hatta kasashen da suka ci gaba, suna ta’ammali da kayayyakin Sin yau da kullum.
Baiwar da Allah ya yi wa Sin ta fuskar yawan jama’a, shi kadai abin alfahari ne, domin kuwa kasuwa ce babba. Yau ko da za a ce Sin ba za ta fitar da kayayyakinta ba zuwa ketare, al’ummar kasar sun isa su samar da babbar kasuwa. Yawan jama’ar da suka kai kusan biliyan daya da rabi ai ba karamar kasuwa ce ba.
Babban abin da ya bai wa Sin nasarar bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri shi ne yadda gwamnati ta maida hankali wajen gina manyan ginshikai da tattalin arziki ke dogara da su domin samun ci gaba mai dorewa. Misali, irin layukan dogon da aka shimfida da suka sada ko wane lungu da sako a duk fadin kasar, da zamanantar da harkar sufurin jiragen sama da na ruwa, gami da bunkasuwar harkar yawon shakatawa ya janyo hankulan kasashen duniya tare da ba su kwarin gwiwa wajen rige-rigen zuwa Sin domin zuba jari.
Tattalin arziki na zamani yana tafiya tare da fasahar zamani, kuma a fannin kirkirarriyar fasaha, kasar Sin tana a sahun gaba. Domin idan ba’a manta ba, a kwanakin baya Sin ta samar da wata kirkirarriyar fasaha mai suna Deepseek, wadda ta bada al’ajabi ga duniya, musamman Turai da America. Har ta kai ga shugaba Trump ya yi kira da a taka birki ga Sin bisa ga yadda take ci gaba cikin sauri a duk fannoni.
Ta fannin inganta rayuwar ‘yan kasa kuwa, Sin ta cike gibin dake tsakanin birane da yankunan karkara. Ma’ana, duk abubuwan more jin dadin rayuwa da za ka samu birni, to akwai su a yankunan karkara. Wannan ya bada damar bunkasar tattalin arziki da zamantakewa masu dorewa a yankunan karkara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp