CRI Hausa" />

Takunkumin Da Amurka Ta Kakkabawa Kasar Sin Wasa Ne Maras Amfani

Ranar 7 ga wata, hukumar kudi ta kasar Amurka ta sanar da kakkabawa wasu jami’an hukumomin gwamnatin kasar Sin masu aikin dake da alaka da yankin Hongkong da wasu jami’an yankin HK takunkumi. Wannan ne karo na biyu da Amurka ta tsoma baki cikin harkokin HK wanda ya kasance harkokin cikin gidan kasar Sin bisa hujjar ’yancin kai, tun bayan da Sin ta gabatar da dokar tsaron kasar Sin dake da alaka da yankin HK. A halin yanzu, wannan doka tana samun karbuwa daga yawancin jama’ar HK, matakin da wasu ’yan siyasar Amurka suka dauka da zummar lahanta tsarin “kasa daya mai tsarin mulki iri biyu” da kuma hana bunkasuwar kasar Sin.
A hakika dai, wadanda aka shigar da su cikin jerin sunayen mutanen da aka kakaba musu takunkumi, mutane ne da suke iyakacin kokarin kiyaye tsaron kasar.
Ana ganin cewa, tun barkewar rikici a watan Yuni na shekarar bara kan gyaran fuska da aka yiwa dokar HK, wasu kasashen ketare suna rurar wutar rikicin ’yan tawaye wajen nuna musu goyon bayan ta da zaune tsaye cikin al’ummar yankin. Kafa dokar tsaron kasar Sin dake da alaka da HK tushen tabbatar da tsaron kasa ne, matakin da sauran kasashe suka gwada sun samu ci gaba mai kyau. Dokar dai ta cika gibin da yankin yake da shi a fannin shari’a, wadda tana taka rawa matuka wajen tabbatar da zaman lafiyar HK cikin dogon lokaci.
Maganar gaskiya ita ce, ’yan tawaye su ne suka illata iko da kuma ’yancin mazaunen HK, dokar tana kokarin maido da zaman rayuwar yau da kullum na jama’ar yankin, mataki ne mafi dacewa wajen tabbatar da doka da shari’a. A yayin taro karo na 44 na kwamiti mai kula da hakkin Bil Adama na MDD da aka yi kwanan baya, kasashe fiye da 70 sun bayyana ra’ayinsu na goyon bayan dokar, matakin da ya bayyana matsayin bai daya da kasashen duniya ke dauka kan wannan lamari.
Babu shakka, wasu ’yan siyasar Amurka ba su son ganin bunkasuwar HK ko kadan, har ma ba su yin la’akari da muradun kamfanoninta sama da 1700 da Amurkawa dubu 85 dake yankin, duk da haka tana son lahanta tsarin “kasa daya mai tsarin mulki iri biyu” da hana bunkasuwar kasar Sin ta yadda za su cimma boyayyen burinsu a siyasance.
Wadannan ’yan siyasar Amurka masu tsananin son kai sun rika tada rikice bisa fakewa da batun HK don cimma burinsu, matakin da ya jefa dangantakar kasashen Sin da Amurka zuwa wani hali mai hadari, har ma ya illata muradun jama’ar kasashen biyu. Sin ba za ta yarda da duk wani matakin da wadannan ’yan siyasa suke yi ba, takunkukmin da suke ikirarin kakabawa tamkar wasa ne ba shi da amfani ko kadan. (Amina Xu)

Exit mobile version