Dan Majalisar da ke wakiltar Gudu/Tangaza a majalisa wakilai, Hon. Sani Yakubu ya bukaci gwamnatin jihar Sakkwato ta bayyana yadda ta kashe naira biliyan uku da gwamnatin tarayya ta bai wa jihar a matsayin tallafin ambaliya.
Dan majalisar na APC ya bayyana cewa, Ministan Kasafin Kudi da Tsare- tsare, Atiku Bagudu ya ce an bai wa jihar Sakkwato naira biliyan uku a matsayin tallafin gaggawa na gwamnatin tarayya domin taimakawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.
- Hedikwatar Tsaro Ta Kulle Birgediya Janar Bisa Zargin Karkatar Da Tallafin Shinkafar Sojoji
- Imanin Sin Kan Ci Gaban Tattalin Arzikinta Zai Haifar Da Tasiri Mai Kyau
Sai dai, dan majalisar ya bayyana cewar, baya ga kananan hukumomin Illela da Tangaza da aka bai wa naira miliyan 30 da miliyan 20 ba su san yadda aka yi da sauran kudin ba, don haka, ya yi kira da cewa, idan kudin hakkin al’ummar Sakkwato ne to a ba su abin su.
Hon. Yakubu wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da sabuwar hukumar bunkasa yankin Arewa Maso Yamma, ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wajen taron kaddamar da rabon takin zamani da Dan Majalisar Dattawa da ke wakiltar, Sakkwato ta Gabas, Sanata Ibrahim Lamido ya jagoranta.
A kan wannan, jam’iyyar PDP a jihar ta bukaci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na EFCC da ICPC da su gudanar da bincike kan zargin da dan majalisar ya yi tare da bayanin abin da aka yi da sauran biliyan 2, 950 kamar yadda kakakin jam’iyyar, Hassan Sahabi Sanyinnawal ya bayyana.