Abubakar Abba" />

Tarairayar Marasa Lafiya: Akwai Bukatar A Ba Ma’akatan Jinya Horo Na Musamman -WHO

Hukumar  kiwon lafiya ta duniya WHO ta koka game da irin yadda sakaci da nuna halin ko-in-kula na ma’aikatan kiwon lafiya ke nuna wa marasa lafiya ke neman ya durkusar da fannin kiwon lafiyar a kasar nan.

Wasumasu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiyasun danganata  sakacin ma’aikatan kiwon lafiya na yin illa ga rayuwar mutane da kuma kawo koma baya a fannin kiwon lafiyar a Nijeriya.

Sun bayuana wasu daga cikin matsalolin da suka hada da,rashin daukarkwararan matakai wajen hukanta likitocin da suka aikata laifuka musamman irin haka da karancin  ma’aikatan nas-nas da rashin  tausayin marasa lafiya da likitoci ke nunawa.

Sauran matsalolin sune,. rashin aiwatar da kudirorin inganta fannin kiwon lafiya da rashin biyan ma’aikatan albashi mai tsoka da kuma rashin horas da ma’aikatan kiwon lafiya da dai sauran su.

A cewar su, baya ga matsalolin da ake fama dasu, akwai kuma rashin kwarewa da horo da wasu ma’aikata basu samu musamman wajen sanin yadda ake tarerayar mara sa lafiya.

Zainab Mohammed masaniyar magunguna dake aiki a asibitin Major Ibrahim dake Zariya, jihar Kaduna ta bayyana cewa rashin kafa dokar da zai hukunta ma’aikatan kiwon lafiya da basu san darajar aikin su ba da kuma rashin sanin hanyoyin da mutum zai bi don kwato hakkin sa idan aka wulakanta shi kokuma cin mutuncin sa a asibiti duk suna daga cikin matsalolin da ake fama da su.

Ita kuwa ma’aikaciyyar jinya a asibitin Gwamna Awan a Kaduna, Margaret Bonat ta ce ma’aikatan kiwon lafiya musamman likitoci da ma’aikatan jinya na iya kokarinsu  wajen kula da marasa lafiya a asibiti.

Babban likitan asibitin Jikwoi Dakta Emeka Anene yace tabas fannin kiwon lafiyar Nijeriya na fama da matsaloli da gwamnati ne kawai za su iya warware wadannan matsaloli.

Ya yi kira ga gwamnati da ta magance wadannan matsaloli da suke fama da su don zai taimaka wajen inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan da kuma kara wa likitocin kwarin  guiwar yin aikin su.

Exit mobile version