Jihadin Shehu Usman Dan Fodiyo
Kasar Hausa ta fara daga kewayen Gobir har ya zuwa gefen kasar Bauchi wadda a da can ake kira da kasar Gobir, wadda kuma a ke kira da tsantsan kasar Hausa (sune kasar Gobir, Zamfara, Kebbi, Katsina, Daura, Rano, Ningi da Kano wanda daga baya ne aka samu kasar Sakkwato) ta faka cikin wani irin nau’in hatsin baran addini, watau na hada bori da addinin Musulunci. A cikin wannan hali da ake ciki na bori, Allah Subhanahu Wata’ala ya karfafa zuciyar Mujaddidi Shehu Usman bn Fodiyo da tsaida sunna, kuma ya karfafa shi da samun nasara wajen fahimtar da jama’arsa.Shehu Usman Mujaddadi ya soma kiran jama’a a mahaifarsa Degel.
Sai dai kamar yadda bayanai a cikin littattafan tarihi suka nuna cewar, Mujaddadi Shehu Usmanu shi kansa bai fita zuwa yake-yake ba sai a wuri daya, watau kasar Gobir da kuma yadda Sakkwato ta samu asali.Littattafan tarihi sun kara bayanin haihuwarsa, cewar an haife shi a watan Safar shekara ta 1168 hijirar Manzon Allah,Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Allah madaukakin Sarki ya kaddara samun Mujaddadi cikin Jama’an Annabi wanda ya kara tsaida addinin Allah da kafafunsa a zukatan Jama’a bayan karkata ta zo masu (kamar a wannan zamani inda kungiyar Izalatul Bidi’a wa’ ikamatussunna ta bayyana mana’ a yau).Yadda al’amari ya kasance kuwa shi ne, inda aka samu ya yi kokarin kawar da ire-iren wadannan shirkoki da bidi’o’i, duk da wasu sai kara kunno kai suke yi.
Shehu Usmanu bai gaza ba musamman ma taimakon Allah da ya samu ta wajen kokartawa har sai da addinin Allah ya daidaitu a zukatan jama’arsa.
Lallai Shehu Usmanu ya amsa sunansa na Mujaddadi kwarai da gaske. Domin ya tsayar da sunna amma kash! mabiyansa sun bijiro da salon son mulki da barna wadda ta fi ta baya. Abin ya kai ga sun kauce wa shari’ar musulunci,na kamanta shi da manzon Allah Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; ko kuma mai da shi abin roko da bautatawa.Haka ma Fulani sun karkata a kan duk wanda bai yi karatu wajen Shehu ba to karkatacce ne,ko da kuwa a ina ya sami ilminsa. Za mu iya samun wannan bayanai ne a wurare da dama da kuma nazarin manufofinsu a zahiri.Amma wasu rubuce-rubucensu na da wuyar samu, musamman yadda su ka farga da cewar jama’a na fahimtar barnarsu ta nazarce-nazarce a kan rubuce-rubucensu da kuma nau’in ayyukansu a zahiri.
A cikin littattafai da ayyuka wasunsu kuwa nada sauyi domin ba a mai da hankali a kansu ba ballantana A Dakatar da su, kuma an mai da su tamkar addinin Allah. Daga cikin wadannan ayyuka da littafai akwai ziyarar kabari da ire-iren shirkoki da bidi’o’in da ke wakana a wuraren, sai littafin Tarihin Fulani na Wazirin Sakkwato, wanda ya rubuta da harsunan Larabci da Hausa. A cikin nazartar littafin zamu iya fahimta barnar tun daga shafi na 8 zuwa shafi na 20 a cikin shi. Misali ya yi bayani kamar haka,”Bushara Da Shehu Usmanu, Allah shi yarda Da Shi:”Hakika bushara an yi da Shehu,Allah shi yarda da shi, tun kafin a san shi, ta abku kamar yadda shi kansa ya ambata cikin littafinsa wanda ya ke maganar kafin bayyanar shi, ta abku kamar yadda shi kansa ya ambata cikin littafinsa wanda yake maganar dangantakarsa zuwa ga Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata gare shi,inda ya ce:“Hakika Annabi tsira da amincin Allah su tabbata gare shi an yo bushara da shi tun gabanin zakuwatai. Ni kuma na gode ma Allah an yi bushra da ni.” Haka kuma zancansa ga dangantakarsa zuwa ga Mahadi.Ya ce: “Hakika Mahadi amincin Allah ya tabbata bisa gare shi, an yo bushara da samu shi. Ni kuma na yi godiya ga Allah an yo bushara da ni…”sauran al’amurra kamar yin masa salati bayan anbaton sunansa kamar yadda ake wa ma’aiki Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da nau’in tsarkakansa kamar na Manzon Allah (S.A.W) watau cewar shi Ma’asumi ne, duba shafi na 9 sakin layi na karke, da dai sauransu. Kamar yadda tarihi ya nuna Shehu Usmanu ya kaurace wa jama’ansa zuwa Gujuba a dalilin irin yadda suka juya wa al’amarin da’awarsa ya zuwa neman abin duniya.