A takaice, abinda cinikin Bayi yayi mana, a matsayinmu na mutane shi ne ya kara inganta hulda tsakanin nahiyar Afirka da yammacin Turai.
Tunda yake dai su Turawan yammacin Turai ba za su iya zuwa wuraren da ake samun ko kamun Bayin, suna dai sayar Bindigogi, Madubi inda har da Giya ga ‘yan nahiyar Afirka wadanda za su iya saye,sai dai kuma kayan da suke sayar masu basu da wani inganci. Saboda irin mutanen sune suke zuwa wurare daban daban domin su nemo masu Bayi. Irin wannan takun na sayen Bayi ko farautarsu yafi hadari a yankin Neja Delta.
- Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (3)
- Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (1)
Daya daga cikin dalilan sune al’ummar Ibo ba a amincewa dasu har zuwa yanzu, domin lamarin daya shafi wani abu, kuwa saboda kuwa lamarin Aro Confederacy wanda wata babbar harkar kasuwanci ce a Arochukwu gabashin Nijeriya wadda tayi babban tasiri kan harkar kasuwanci a yammacin Afirka, bama kamar a cikin karni na 18 dana 19, inda aka wata babbar ce bugu da kari idan dai ana maganar harkar kasuwanci ta hada duk wadansu wurare da suke kusa da gabar ruwa,inda suka kasance tamkar wasu dalilai tsakaninsu da Turawan mulkin mallaka, musamman ma alamarin daya shafi cinikin Bayi.
Idan ana maganar tsantsan gaskiya kuma su ma ‘yan nahiyar Afirka sun nuna turjiya dangane da lamarin cinikin Bayi. Matsalar bata wuce ace lokacin da aka fara nuna turjiya din an riga an makaro wato wankin hula ya kai dare ke nan. Domin kuwa Lloyd ya nuna cewa tsakanin 1689 da1807, an samu damar lalata kashi 17 na jiragen ruwa wadanda su bayin ne suka yi hakan tare da taimakon jama’ar gari.
Lamarin cinikin Bayi a Afirka ya canza saboda yadda ake tafiya da Bayin da aka saya a kai su waje ta jirgin ruwa, ba domin komai ba sai saboda an yi amfani da cinikin Bayin ne saboda kawai a samu damar maida muatnen da aka saya Bayi su rika yin ayyukan bauta. Wadansu daga cikin mutanen da sun rika sayar da ‘ya’yan makwabtansu suna maida su Bayi. Yayin da wasu kuma suna sayar da makwabtan nasu ne.
Al’ummar Aro, Edo da kuma Ashante ko shakka babu sune wadanda suka fi dacewa ayi kwatance da su,domin sune suka maida wuraren da makwabtansu wuraren da jigilar Bayi.Irin haka ne yasa, ‘yan kabilar Efik basu amincewa Igbo yayin da su kuma (Aro), Esan basu yarda da Edo ba,hakanan su ma, Ewe har zuwa yanzu amincewa Asante ba a kasar Ghana.
Duk da yake an samu tsaiko na shekara 50 wato kafin su Turawan mulkin mallaka su sake dawowa su yi mana mulkin mallaka, sai dai, a wancan lokacin akwai wadansu abubuwan da aka yi shekarun da suka gabata. Kasar ko daular Benin ta samu ja da baya, ‘yan gudun hijira sun tsere daga Jihadin Sakkwato,tsofaffin Bayi kamar irinsu Samuel Ajayi Crowther ya dawo gida Nijeriya amma fa da ilimin zamani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp