• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Taron Ƙasashen Musulunci A Saudiya: Tinubu Ya Nemi A Kawo Ƙarshen Ta’addancin Isra’ila A Gaza

by Sulaiman
11 months ago
Gaza

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci a kawo ƙarshen hare-haren ƙare-dangin da ƙasar Isra’ila yi wa Zirin Gaza, yana mai jaddada cewa tsawaita rikicin da take yi a Falasɗinu ya janyo wahala mai yawa.

 

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a babban taron ƙasashen Larabawa da Musulmi da aka gudanar a Riyadh, babban birnin ƙasar Saudi Arebiya, inda shugabannin suka taru domin magance matsalar da ke ƙara ƙamari a yankin Gabas ta Tsakiya.

  • Taron Ƙasashen Musulunci A Saudiya: Tinubu Ya Nemi A Kawo Ƙarshen Ta’addancin Isra’ila A Gaza
  • ACF Ta Bukaci Sojoji Su Gaggauta Murkushe Lakurawa

A yayin da yake jawabi ga shugabannin Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmi (OIC) da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa, Tinubu ya bayyana goyon bayan Nijeriya na ganin an samar da maslaha tsakanin ƙasashen biyu.

 

LABARAI MASU NASABA

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

Ya yi kira da a samar da wani ƙudiri da zai bai wa Isra’ila da Falasɗinawa damar zama tare cikin lumana da tsaro.

 

Ya ce: “Rikicin na Falasɗinu ya daɗe da daɗewa, yana jawo wahala mai yawa ga rayuka,” in ji shi.

 

Shugaban na Nijeriya ya jaddada cewa tofin Allah-tsine ake yi kan lamarin bai isa ba, yana mai kira ga shugabannin duniya da su tashi tsaye don kawo ƙarshen abin da Isra’ila ke aiwatarwa a Gaza.

 

Ya ce: “Babu wata manufa ta siyasa, da dabarun soji, da kuma matsalar tsaro da ya kamata ta kawo asarar rayuka da dama,” inji shi.

 

Ya yi kira ga dukkan ɓangarorin da ke rikici a Gabas ta Tsakiya da su kiyaye ƙa’idojin daidaito da haƙƙoƙin fararen hula a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.

 

Shugaban ya yaba wa Sarki Salman na Saudiyya da kuma Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman bisa kiran taron, yana mai bayyana shi a matsayin wata muhimmiyar dama ta sabunta yunƙurin diflomasiyya da ƙoƙarin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

 

Ya ba da tabbacin cewa Nijeriya za ta ci gaba da tallafa wa yunƙurin ƙasashen duniya na haɓaka zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya.

 

Shugaba Tinubu ya buƙaci da a kafa sakatariyar da za ta aiwatar da ƙudirorin taron.

 

Ya buƙaci shugabannin da su umarci zaɓaɓɓun shugabannin gwamnatocin da su nemi tallafi a duniya da kuma sa ido kan aiwatar da ƙudirorin taron, tare da bayar da rahotanni a kai a kai ga shugabannin ƙungiyar OIC da na Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa, har sai an samu zaman lafiya na dindindin a yankin Gabas ta Tsakiya.

 

A jawabin sa na buɗe taron, Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya yi Allah-wadai da ta’addancin da Isra’ila ke yi a Gaza da Lebanon, da suka haɗa da kai hari kan fararen hula da kuma ci gaba da keta haddin masallacin Al-Aƙsa.

 

Ya kuma yi Allah-wadai da haramcin da Isra’ila ta yi wa Hukumar Ba da Agaji da Ayyuka ta amfani Majalisar Ɗinkin Duniya (UNRWA) daga kai kayan agaji ga Falasɗinawa da kuma raba al’ummar Lebanon da muhallin su da take yi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya
Da ɗumi-ɗuminsa

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna
Manyan Labarai

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

October 18, 2025
Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi
Manyan Labarai

Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi

October 18, 2025
Next Post
Wakilin Musamman Na Sin Game Da Batun Sauyin Yanayi Ya Yi Karin Haske Game Da Shigar Kasarsa Batun Shawo Kan Sauyin Yanayi

Wakilin Musamman Na Sin Game Da Batun Sauyin Yanayi Ya Yi Karin Haske Game Da Shigar Kasarsa Batun Shawo Kan Sauyin Yanayi

LABARAI MASU NASABA

gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
ASUU

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025
Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.