‘Yan sama jannatin kasar Sin na kumbon Shenzhou-14, sun fara tattakin da aka tsara zai kai na sa’o’i 7, a wajen tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, tun daga karfe 6:26 na yammacin Alhamis din nan, bisa agogon birnin Beijing, daidai da karfe 10:26 agogon GMT.
Dan samajannti Chen Dong ne ya bude kofar fita, ta bangaren dakin binciken samaniya na Wentian dake tashar ta samaniya. Kana Chen Dong da Liu Yang suka fita wajen dakin, yayin da Cai Xuzhe ke tallafa musu da wasu hidimomi ta cikin tashar.
Ana sa ran ‘yan sama jannatin za su dasa karin wasu fanfuna, su kuma daga kyamara mai jujjuyawa dake saman dakin binciken. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp