A wannan makon dai Nijeriya ta dauki dumi dangane da batun haramta amfani da taliyar ‘yan yara a cikin kasar bisa zargin tana dauke da sinadaran da ke haddasa cutar kansa.
Lamarin ya jefa ‘yan Nijeriya da dama cikin rudani duba da yadda suka shafe tsawon shekaru suna dura wa cikinsu wannan taliyar, musamman wadanda suke yawan ziyartar wuraren masu sayar da shayi, inda ake musu hadin ta da kwai domin kashe yunwa ko don kwadayi.
Ita dai hukumar kula da ingancin kayayyakin abinci da maguna a Nijeriya (NAFDAC), ta fito ta shelanta haramta shigowa da amfani da taliyar Indomie da ake shigowa da ita cikin Nijeriya bisa zargin tana haifar da cutar kansa ga masu amfani da ita.
A kwanakin baya ne, jami’an kiwon lafiya na kasar Malaysiya da na Taiwan suka gano cewa taliyar ta ‘yan yara na dauke da sinadarin da ake kira ‘Ethylene Odide’ da ke haifar da cutar kansa. Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Malaysiya ta ce, kusan sau uku ana gudanar da bincike kan samfurin Indomie kuma na nuni da cewa taliyar na dauke da wannan nauyin sinadarin.
Da take magana kan wannan matakin, Darakta Janar ta hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta shaida cewar hukumar za ta fara gudanar da gwaje-gwaje kan samfurin wanda ake shigo da ita daga waje domin kara gano hakikanin gaskiyar lamarin.
Adeyeye da take magana a ranar Litinin, ta ce hukumar NAFDAC ta farka kan lamarin tare da fara bincike tun lokacin da ta samu bayanai daga hukumomin kiwon lafiya na kasar Taiwan da Malaysiya.
A cewarta, NAFDAC za ta shiga farautar taliyar da aka haramta a cikin kasuwanni domin tabbatar da cewa wasu bata-gari ba su fasa shigo da shi cikin kasar nan.
“Za mu yi gwajin samfurin taliyar ‘yan yaran har da dandanonsa tun daga sarrafa shi har zuwa matakin bibiyar kasuwanni.
Sakamakon bullowar sinadarin ‘ethylene odide’ mun shigo da kwararru da za su yi mana nazarinsa.”
Ta ce ba wannan ne karo na farko da aka taba haramta amfani da tafiyar kasar waje a kasar nan ba, tana mai cewa tuni gwamnatin tarayya ta hana shigo da shi kuma bai da rajista da NAFDAC.
Ta kara da cewa taliyar ‘yan yaran ta kasashen waje tun shekarun baya tana daga cikin nau’ikan abinci da gwamnatin tarayya ta haramta amfani da ita.
Sai dai kuma, daraktan ta fayyace zare da abawa, inda ta ce Indomie da ake sarrafawa a Nijeriya su kam suna da inganci kuma ba a haramta amfani da su ba, kan hakan ta ce suna da rajista da hukumar don su ba su dauke da sinadarin da ke janyo kansa.
Hukumar NAFDAC ta nemi al’umma da su gane cewa Indomie da ake sarrafa su a cikin Nijeriya ba su da alaka kwata-kwata da wadanda ake yinsu a kasar Malaysiya da ta Taiwan.
Ta kara da cewa, “Akwai bukatar jama’a su sani cewa taliyar ‘yan yaran tun shekarun baya daman gwamnatin Nijeriya ta hana shigo da shi cikin kasar nan. Bugu da kari, bai da rajista da hukumar NAFDAC,” ta bayyana.
A cewarta, tun lokacin da suka samu bayanai daga hukumomin kasar Taiwan da Malaysiya suka tashi tsaye wajen fara bibiyar sawun taliyar ‘yan yaran. Ta nanata haramcin shigo da taliyar sun yi ne da nufin kare lafiyan al’umman kasa domin tabbatar da cewa abincin da suke ci bai da illa a garesu.
Hakazalika, ta ci gaba da cewa yin hakan wani mataki ne na tabbatar da cewa ba a yi fasa kaurin shigo da taliyar cikin kasar nan ba. Sai ta gargadi masu kokarin shigo da taliyar ta barauniyar hanya da cewa ka da ma su fara domin hukumar za ta sanya ido, kuma za su bibiyi hatta kasuwanni wajen tabbatar da an daina shigo da shi balle a sayar.
Ita ma dai hukumar lafiya ta birnin Taipei na kasar Taiwan, ta shelanta wa duniya cewa ta gano cea akwai sinadarin ‘ethylene odide’ da ke haddasa cutar kansa a cikin taliyar ta ‘yan yara, don haka ta nemi jama’a da su yi hattara.
Saboda haka, ma’aikatar lafiya ta Malaysiya ta ce sun yi gwaje-gwaje a kan taliyar ‘yan yara guda 36 na kamfanoni daban-daban tun daga 2022, kuma sun gano cewa samfura 11 na dauke da sinadarin.
Sai dai Malaysiya ta ce ba ta dauki matakin ba ne domin musguna wa wadanda abun ya shafa, sai dai ta yi haka ne domin ceto al’umma gaba daya.
Kasashen biyu sun bayar da umarnin cewa ‘yan kasuwarsu su fitar da taliyar ta daga cikin shagunansu nan take, kuma su kauce wa amfani da su.
Shi kuma kamfanin Indofoods da ke Indonesiya mai sarrafa taliyar ‘yan yara, ya fito ya karyata zargin kasashen biyu da ke cewa taliyar na dauke da nau’in sinadarin. Ta kuma ce tana da cikakkiyarn shaidar a kan matakinta.
Mista Taufik Wiraatmadja, mamba ne a majalisar daraktocin kamfamnin Indofoods, ya kare kamfanin da cewa suna kiyaye inganci da kiwon lafiya sosai wajen sarrafa taliyar.
Mista Wiraatmadja ya kara da cewa kamfanin na da shaidun gudanarwa kuma nagartattu wadanda suka samu daga hukumomin kula da abinci na duniya.
Ya nuna mamakinsa kan yadda aka yi rufdugu kan taliyar a ‘yan kwanakin nan, domin suna daga cikin kamfanonin abinci da ke fitar da abin da suke sarrafawa a kasashe sama da 90 cikin har da Saudiyya da Nijeriya, kuma suna bukatar gamsuwa da abun da suke fitarwa.
Sai dai duk da hakan, masana na nuni da cewa al’ummar Nijeriya na cin taliyar ‘yan yara fiye da tunani. Kididdiga ta yi nuni da cewa kasar tana daga cikin manyan masu kawo wa kamfanonin sarrafa taliyar ‘yan yara riba mai tsoka.
Wasu masana na kallon wannan matakin tamkar zai taimaka wajen bunkasar kamfanonin da suke fitar da Indomie a Nijeriya, kuma tamkar mataki ne da tattalin arzikin kasar zai kara habaka domin za a samu karin masu sayen abincin da ake sarrafawa a cikin kasar nan ba wai na kasashen waje ba.