Bankin raya kasashen Afirka ya ce zai yi wahala nahiyar ta murmure daga koma bayan tattalin arzikin da duniya ta fuskanta, muddin aka ci gaba da gindaya wa kasashen nahiyar ka’idoji masu tsauri fiye da sauran kasashe kafin a ba su rancen kudi.
Shugaban bankin na AFDB, Akinwumi Adesina, ya ce kasashen Afirka na fuskantar kalubalen rashin yi musu adalci wajen ba su bashin ne, duk da cewar suke kan gaba wajen bukatar masu zuba hannun jari, domin magance matsalolin sauyin yanayi ta hanyar bunkasa hanyoyin samar da makamashi maras gurbata yanayi.
- Gwamna Lawal Ya Jagoranci Taron Majalisar Zartaswa Kan Tattara Kudin Fansho
- An Kashe Basaraken Taraba, An Sace Matarsa, Dansa Da Wasu 8
Adesina ya yi wannan gargadi ne a lokacin da yake gabatar da jawabi ga mahalarta wani taron masu ruwa da tsaki kan tattalin arziki, wanda ya gudana ta kafar Intanet.
Shugaban bankin, ya kara da cewar: “Duk wata nahiya ko yanki na duniya na iya fuskantar matsalolin da suka hada da yunwa, rashin jagoranci nagari, rashin tsaro, barkewar annoba, nauyin bashi da kuma sauyin yanayi, sai dai nahiyar Afirka ce ke kan gaba wajen shan wahala, la’akari da dogaron da ta yi wajen sayen akasarin kayayyakin da ta ke bukata daga kasashen ketare saboda rashin ci gaban masana’antu.”
Wani rahoton masana dai ya bayyana cewar yanzu haka mutane akalla biliyan biyu da miliyan 300 ne ke fama da yunwa a sassan duniya, matsalar da Akinwumi Adesina ya ce ya zama tilas kowace kasa ta bayar da gudunmawa wajen magance ta.