Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NIMASA) ta ce, ‘yan Nijeriya mutum miliyan 350 za su samu cin gajiyar samun damar ayyukan yi da kasuwancin dala tiriliyan 2.5 a duk shekara muddin aka yi amfani da harkokin tattalin arzikin cikin tekunan ruwa yadda ya dace.
Daraktan gudanarwa NIMASA, Bashir Jamoh, shi ne ya shaida hakan a Jihar Legas yayin wani taron horaswa da cibiyar bayar da hoto ta kasa da kasa ta shirya da hadin guiwar hukumar ga ‘yan jarida, ma’aikatan jiragen ruwa da kuma jami’an tsaron tashoshin jiragen ruwa.
- ‘Yan Adawa Sun Dana Wa Ministar Mata Tarko – Gwamnatin Kaduna
- Dokar Fallasa Barayin Gwamnati Na Nan Daram – Gwamnatin Tarayya
Da yake magana dangane da makoma a nan gaba, Jamoh ya kara da cewa akwai bukatar tabbatar da tsaro a mashigar tekun Guinea (GOG), yana mai cewa ta hakan na da muhimmanci ga ci gabab tattalin arziki ma’adinan ruwa da kuma kasashen da ke gabar teku a yankin.
Ya tabbatar da cewa, Nijeriya za ta yi duk mai yuwuwa wajen kare iyakarta da GOG.
“Dole ne gwamnatin tarayya ta bullo da tsare-tsaren kasafin kudi da za su taimaka wa fannin ci gaba. Tattalin arzikin halittun da ke cikin tekuna za su iya samar da ayyukan yi guda miliyan 350 da tara dala tiriliyan 2.5 a duk shekara, don haka akwai bukatar Nijeriya ta sanya himma a wannan bangaren domin tabbatar da an ci gajiyasa yadda ya dace.
“Aikin gidajen yada labarai ne wayar wa ‘yan Nijeriya kai dangane da muhimmanci da fa’idar da ke tattare da tattalin arzikin halittun da ke cikin tekunan ruwa, kuma ‘yan jarida ne za su maida hankali ga kasashen duniya,” Jamoh ya shaida.
Daga bisani, ya yi kira ga ‘yan jarida da su daina yada munanan rahotonni a kan filayen jiragen ruwa da kuma mashigar iyakar Guinea.