Lokaci ne na kula da jariri ba don wanka jego ba, da yanzu watakila mutum ko ganuwa ba zai yi ba ballantana ya dauki kansa a hoto. Domin kuwa kaina ya mole a lokacin da ake ciro ni daga cikin mahaifiyata. Amma cikin ikon Allah, kaka ta Ita ta rika gyara kan nan, tana gasa shi har sai da ya koma inda yake. Haka nan ana haifar yaro ya zo da matsalar cibi. Wato cibiya ta ki faduwa, su manya sun san yadda ake yi don ta fadi da sauri, idan ba ka bari an yi wa yaro ba zai cutu.
Lokaci ne na gyara, lokacin haihuwa gaban mace yana karuwa, wani lokacin ma sai an yanka wajen don yaro ya samu kofar fita wadatacciya. Su manyan mu sun san duk wata dabara da ake yi don gyaran wajen da kuma mayar masa da armashinsa don jin dadin maigida. Idan ba a yi haka ba, to kai ma ba za ka ji dadin saduwa ba.
- Abubuwan Da Za Su Taimaka Wa Mai Azumi Ya Kasance Cikin Koshin Lafiya
- Kula Da Fata Mai Maiko Da Ke Bata Kwalliya
 Lokaci ne na inganta lafiya a wannan lokacin ne ake ba wa uwargida duk wani nau’in abinci irin su sabaya, kunu, da sauran su don kara mata lafiya, da kara lafiyar mama don yaro ya samu ya sha. Ina da sani akan wannan, za ku ga wadanda suka haihu ba a Nijeriya ba suna samun matsaloli da dama kamar rashin ruwan mama wanda yaro zai sha kuma yana da kyau yaro kar ya fara da komai sai da ruwan nonon babarsa saboda yana da amfani sosai a jikinsa.
Lokaci ne na hutu, bayan haihuwa mace tana bukatar hutu. Hutu daga kicin, daga hidimar gida, da sauransu. Idan ba ta samu hutun da ya dace ba, to za ta iya lalacewa, jikinta ya sakwarkwace kamar tsohuwar mota musamman ma idan haihuwa ta zo da CS. Dole ta huta, dole a kula da ita.
Illolin tafiya gida wanka Jego
Yana bude kofofin matsala bincike da bayanai na masana matsalolin aure ya tabbatar da cewa da yawa daga cikin maza wanda su kan tsinci kansu a cikin matsalar neman mata banza ya samo asali ne a lokacin da matan su suka tafi gida wankan jego.
Wani namijin ko da baya harkar banza, ganin ya samu sarari, ya kan dauki sabbin dabi’o’i irin su neman mata, shaye-shaye da sauran su.
Rashin samun mai kulawa da shi, kamar abin da ya shafi abincinsa, da sauran hidimomi, ya kan sa ya nema ta hanyar da bai dace ba.
Wani ma daga nan yake koyon dabi’ar zuwa hira majalisa ko zuwa gidajen kallo da sauran su.
Haka nan zuwa jego gida, yana haifar da zargi, domin kuwa, ita uwangida da zarar ta ga canji, za ta fara kawo abubuwa akanta, daga karshe sai ta rika zargin ya shiga cikin zamantakewar.
Bugu da kari, yana haifar da rashin lafiya, mata da yawa sun kamu da ciwon sanyi da ciwon hawan jini a sakamakon wanka jego. Yanayin wanka yana sanya jini ya hau. Don haka ma likitoci da dama suke hanawa. Amma idan da za a yi da kyau, to za a iya toshe wannan matsala.
za mu ci gaba mako zuwa idan Allah ya kai mu