Tattaunawar Musamman Da Saratu Gidado (Daso) Da Ta Shera 21 A Kannywood

Saratu

Shafin yau ya yi maku babban kamu inda ya zakulo maku mashahuriya wadda ta ga jiya ta ga yau a masana’antar Kannywood wato HAJJIYA SARATU GIDADO wadda aka fi sani da suna DASO. Babbar Jarumar da ta shekara ashirin da daya 21, tana ba da gudunmawarta a cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa. Ta bayyana wa masu karatu dalilin da ya sa har ta karkata ga shiga harkar fim, ga dai yadda hirar ta kasance tare da FURODUSA YAKUBU BALA GWAMMAJA:

 

Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanki tare da dan takaitaccen tarihinki…

Sunana Saratu Gidado wadda duniya tafi fi sani da sunan Daso ta hausa fim, Ni ‘yar asalin jahar kano ce cikin tsakiyar kwaryar birnin jihar kano ni ‘yar Nigeriya ce, Alhamdulillah ni musulma ce bahaushiya. Na yi karatun firamare da sakandare da haya instushon, a kaduna ‘polytechnic’, na karanta ‘Business administration’, daga nan sai na tafi london na yi satifiket kos, a makarantar ‘Polytechnic of north london’, na wata tara na karanta kos din Human ‘psychology’ ma’ana dabi’ar dan adam, bayan na dawo na yi aure ina da iyali daga nan sai na shiga koyarwa a firamare sikul kuma, bayan ina koyarwa a firamare sikul kuma sai aurena ya mutu toh bayan aurena ya mutu kuma sai na shiga harkar fim daga firamare sikul, na shigo harkar fim a shekara ta 2000 ta kamfanin sarauniya fim furodukshin, fim din su da suka fara sani shi ne ‘Linzami da wuka’, anan ne na samu suna Daso, daraktan sarauniya fim din Allah ya ji kanshi Aminu Muhammad Sabo wanda nake tsokanarsa Tsigi Tsila, tom daga nan kuma sai suna ya bini duk fim Daso, duniya ma ta dauka ta bini da suna Daso. Toh bayan nan kuma na yi fina-finai da yawa wanda tun ina kirgawa gaskiya wallahi yanzu ma ba zan iya kirga wasu ba, toh Alhamdulillahi shi ne dai tarihin rayuwata a takaice kenan ba wai ‘In Full’ ba.

 

Me ya ja hankalinki har kika tsunduma cikin harkar fim?

Abinda ya jaho hankalina na shiga harkar fim shi ne, toh wanda ke koyarwa a firamare sikul kananan yara suna karuwa da ilimin da Allah ya yi mini sai nagamanya kuma ta ina za su karu tare da ita a lokaci guda sai na ga har kar fim ita ce ana sawa ana kallo da babba da yaro duk za a karu da ilimi da baiwar da Allah ya yi min, toh shi ne sai na shiga harkar fim, gaskiya wannan ne dalili kam ba na tsaya yara kadai su karu dabasirar da Allah ya yi min ba sai na ga gwara har da manyan ma, tunda harkar fim kallonta akwai fadakarwa, akwai ilmantarwa, akwai wasa, akwai dariya, akwai nishadantarwa, akwai barkwanci, duk dai abinda Allah ya kawo na alheri duk dai muna yi a harkar fim, toh wannan ne dalilin da ya sa nace bari na yi harkar fim, manya da yara duka lokaci guda su karu da shi.

 

Wacce irin gwagwarmaya kika sha wajen shiga cikin masana’antar?

Ban samu wata Gwagwarmaya ba, na shiga harkar fim, Kuma wadanda na samu a ciki gaskiya sun karbe ni hannu bibbiyu. Allah ya jikan Hajiya Hauwa Ali Dodo, Ubangiji Allah ya saka mata da alkhairi, ta karbe ni hannu bibbiyu mun hadu da ita a Sarauniya wajen shutin fim din gaskiya ta karbe ni hannu bibbiyu sosai, har tana koya min yadda zan yi wani aktin din fim din wallahi na yi mamaki kwarai da gaske ba ta da kishi ba ta da damuwa da mutum in ya zo sabo. Tana dora shi a kan harkar wannan dai ba zan manta da ita ba, sai Lubabatu Madaki ita ma hannu bibbiyu ta karbe ni dan su na samu a sarauniya fim furodukshin, hannu biyu itama ta karbeni wallahi gashi har yanzu muna da ran mu da lafiyarmu ni da ita kuma ci gaba da mutuncin mu, toh wannan shi ne sai dan abinda ba a rasa ba da wasu can wanda ni nama manta in ba yanzu da aka yi min maganar ba.

 

Lokacin da kika je da maganar sha’awar shiga harkar fim gida,ko akwai wani kalubale da kika fuskanta ganin yadda a lokacin ba kowa ne ya fuskanci fim ba, musamman ke da kike ‘yar babban gida,me za ki ce akan hakan?

Ai daman ai dole in abu ya zama sabo a gurin mutum sai ya samu gwagwarmaya dangi kam musamman ma mahaifiyata lokacin tana da rai Allah ya ji kanta, Allah yasa ta huta, tunda kauye take lokacin da zama ta ce “Saratu wannan harkar da kika shiga ta fim ko za ki daina? dangina suna ta cewa wai na barki kin shiga wasan hausa” na ce “ki yi min addu’a harka ce me kyau sana’a ce kammar yadda kowa yake ji da sana’arsa, itama wasan hausa abar ji ce, kuma kowacce sana’a akwai nagari akwai bata gari a kowacce sana’a, toh ni in Allah ya yarda na shiga da kyakkyawar niyya, kuma za mu ji dadi gaba dayanmu ni da su, za su samu alheri in Allah ya yarda in na samu a harkar, kuma bana fatan samun akasin alherin, saboda haka ta ce “toh shikkenan ba wani abu Allah yasa kin shiga a sa’a da alkhairi ina yi miki fatan alkhairi, toh wannan addu’ar da mahaifiyata ta yi toh ta kara min kwarin gwiwa ta harkar, shiyasa nake ta ci gaba. Gaskiya fisabilillahi na kwantar mata da hankali na nuna mata ni babbace fa ba yarinya bace tunda sai da na yi auren fari sannan na shiga harkar fim, toh dan haka san ‘Im matual enough’ me hankali ce ni wadda ba za a yaudareni ko wani abu ba, toh wannan shi ne. Kuma daman ko addini da ya zo mana gaskiya sai da ya samu kalubale iri-iri so haka karatun boko da ya fara zuwa kasar da ma afrika gaba daya an samu kalubale a komai ai daman akomai ‘in general’ sai an sami kalubale sai kuma daga baya a gano alherin abun, toh wannan shi ne.

Duk da cewa fina-finan da kika yi na da yawan da ba za ki iya kidayasu gaba daya ba, ko za ki iya kintatar yawansu ki fadawa masu karatu?

Ina! kirga fina-finai ai da wahala, shekarata fa ashirin da daya a fim indosturi, ka ga kuwa ai zai wuya in kirga tun ina kirgawar har na daina ba zai yu ba, zai wuya, tunda wani fim din sin daya za ka yi, kuma kaga dole za a ce wance da ita a fim ka za, ka ga kuwa ai yaushe, wani fim labari akanka, wani fitowa goma, wani fitowa biyar, gashinan dai gaskiya ba zan iya rukewa ba, wallahi ba zan iya ba.

Zamu ci gaba mako me zuwa

Exit mobile version