Daga Abdulrazaƙ Yahuza Jere
Jarumar fina-finan Indiya Juhi Chawla ta yi wani kyakkyawan abishir ga masu kallo cewa fim ɗin da za ta fito na gaba zai kasance mai motsa zukata tare da nuna rayuwar iyali mai daɗi.
A cewarta, “Zan fara ɗaukan fim ɗin a watan Disamba mai zuwa. Zai ƙayatar da masu kallo saboda yadda aka tsara kalaman ciki. Bari dai kar in shanye muku daɗin tun yanzu, saboda za a sanya ranar da za a yi sanarwar musamman game da fim ɗin. Sai dai kawai in ce ku sha kuruminku, ina tabbatar muku da cewa fim ɗin zai ƙayatar da ku”, in ji ta.
Fim na ƙarshe da jarumar ta fito a ciki dai shi ne “Chalk n Duster”, kana ba ta bayyana sunan sabon fim ɗin nata ba.