Kwanan baya, rukuni na 26 na tawagar sojin injiniya ta wanzar da zaman lafiya ta kasar Sin sun sami iznin MDD a cikin bincike da ta yi na rubu’i na biyu kan na’urori, inda suka tafi lardin Kivu ta Kudu, da ake fama da bala’in ambaliyar ruwa, don gudanar da aikin ceto.
Tawagar ta tura sojoji 30 don gudanar da aikin ceto a lardin, wanda ya yi fama da ambaliyar ruwa a watan da ya gabata.
Sojojin 30 za su shimfida wata gada kan muhimmiyar hanyar zuwa wuraren da bala’in ya shafa. Shugaban sojojin Xiong Dingda ya nuna cewa, ko da yake ana fuskantar matsaloli wjen shimfida gadar, amma takwarorinsa za su daidaita duk wata matsala don kammala aikin, da bude wata hanyar sufurin kayayyakin jin kai cikin hanzari.
A tsakiyar watan Mayu ne, an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a lardin na Kivu ta Kudu, inda bala’in ya haddasa asarar rayuka fiye da 400, tare da bacewar mutane a kalla dubu 5. Ya zuwa yanzu, hanyoyin shiga wannan wuri na toshe. (Amina Xu)