Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake neman ‘yan kasa da su kara hakuri da tsare-tsarensa na farfado da kasa, yana mai cewa, yana sane da yadda mafi yawan ‘yan Nijeriya ke fama da tsayar kayayyakin rayuwa da suka samo asali daga tsare-tsaren gwamnatinsa.
Tinubu wanda ke wannan bayanin a ranar Talata cikin jawabin da ya gabatar wa al’umma na ranar samun ‘yancin kai na shekaru 64 da suka gabata.
- Daga Yanzu Saudiyya Ce Za Ta Kula Da Abincin Alhazan Nijeriya -NAHCON
- Dimokuradiyyar Jama’a Da Ta Shafi Matakai Daban Daban Wani Muhimmin Tabbaci Ne Ga Ci Gaban Kasar Sin
A cewarsa, a halin da ake ciki, gwamnati mai ci tana kokarin yadda za a samu shawo kan matsaloli ne masu dorewa ba wai na ‘yan kankanin lokaci ba.
Tinubu ya ce, nan ba da jimawa ba jama’a za su dara domin kuwa a halin yanzu gwamnati na tafiyar da wasu tsare-tsaren da manufofin da za su rage tsadar rayuwa da ake ciki da kawo sauki ga matsin da ake ta kuka.
Shugaban ya kara da cewa, gwamanti za ta yi duk mai yiyuwa wajen ganin ta shawo kan matsin rayuwa da jama’a ke ciki da kuma hauhawar farashin kaya tare da duba wasu manufofin da suke wahalar da jama’a.
Tinubu da kansa ya amince kan cewa yanzu dai babban damuwar ‘yan kasa shi ne, matsin rayuwa da tsadar kayan masarufi, musamman na abinci.
“Babban abun da ya fi damun mutanenmu a yau shi ne, tsadar rayuwa, musamman kan kayayyakin abinci. Wannan lamarin ya shafi mutane da dama a fadin duniya, inda farashin da tsadar rayuwa ke ci gaba da faruwa a fadin duniya.
“Ya ku ‘yan Nijeriya, ina mai tabbatar muku da cewa muna aiwatar da manufofi da dama da za su kai ga daukar matakai rage tsadar rayuwa da ake fuskanta a gidaje.”