Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya ce babu wani mutum da zai iya daukar nauyin Nijeriya shi kadai, sai da taimakon Allah.
Gbajabiamila ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a ranar Laraba bayan sallar Idi a Legas.
- Ku Zubar Da Rayuwar Ikirari Don Ci Gaban Nijeriya – Sultan Ga Shugabanni
- Kungiyar Al-Ahli Ta Saudiyya Ta Sayi Golan Chelsea, Mendy
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ya roki ‘yan Nijeriya da su rika yi wa Tinubu addu’a.
“Lokaci ne mai wahala ga Nijeriya amma za mu shawo kan komai. Abin da shugaban kasa ke bukata a gare ku yau da gobe shi ne addu’arku.
“Nauyin Nijeriya ba shi ne nauyin da kowane dan adam na yau da kullun ko na talaka zai iya dauka ba sai da taimakon Allah Madaukakin Sarki.
“Don haka a bayyane yake cewa Allah Ta’ala yana tare da shugabanmu. Yana dauke masa nauyi,” in ji Gbajabiamila.