Shugaban hukumar tsaro a Kasuwanci ta Nijeriya (SEC), Emomotimi Agama, ya bayyana cewa shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya amince da masana’antar cryptocurrency kafin shugaban ƙasar Amurka mai jiran gado, Donald Trump.
Agama ya bayyana wannan ne a yayin wani taron kasuwanci na masana’antar kuɗi na Afirka da aka gudanar a Casablanca, Morocco, inda ya ce, a lokacin da aka naɗa shi a matsayin shugaban SEC, shugaban ƙasa ya goyi bayan wannan masana’anta, saboda dangantakarsa mai kyau da masana’antar.
- Waƙa Sana’a Ce Sai Da Ilimi Da Jari -Wizzamany
- Yana Da Kyau Matasa Su Rika Shiga Harkar Kudaden Crypto – Farfesa
A cikin amsarsa game da manufofinsa na halartar taron da kuma hangen nesan 2025, Agama ya ce, “Abin da ya sa na zo Casablanca shi ne dalilin da ya sa kowa ya zo. Hadakar kasuwannin jari da tsarin kuɗi na Afirka don zama hanya ɗaya wacce za ta iya samar da sabis ga kowanne ɗan Afirka daga kowanne ɓangare.”
Agama ya bayyana cewa gwamnati yanzu ta yi abin da ya kamata wajen amincewa da cryptocurrency, yana mai cewa ya kamata a yaba wa shugaban ƙasa Tinubu saboda amincewarsa da cryptocurrency kafin Donald Trump a Amurka.
“Zan fara ba da yabo ga shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, don naɗa ni da ya yi a SEC, kuma yana daga cikin masu sha’awar cryptocurrency,”
inji Agama.