Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar da wani babban asibiti mai gadaje 300, da Bas 100 na masu amfani da CNG, da sauran ayyukan da gwamnan Kaduna Uba Sani ya kammala a ranar Alhamis.
Asibitin da aka ƙaddamar an fara gina shi ne a lokacin tsohon gwamnan jihar kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo. Tinubu ya kuma ƙaddamar da cibiyar bayar da Horar a Rigachikun, da hanyar Kauru-Pambegua mai tsawon kilomita 25, da kuma wasu wuraren kula da lafiya a Tudun Biri.
- Gwamnonin APC Sun Nemi Tinubu Ya Ƙirkiri ‘Yansandan Jihohi Don Yaƙar Matsalar Tsaro
- APCn Kaduna Ta Mara Wa Tinubu, Uba Sani Da Kakakin Majalisa Abbas Baya Don Wa’adi Na Biyu
A yayin liyafar da aka yi bayan ƙaddamar da ayyukan, Shugaba Tinubu ya yaba wa Gwamna Sani saboda yin ayyukan da suka dace da buƙatun jama’a. Ya bayyana cewa yana farin cikin yanayin zaman lafiya da ke kaduna, wanda ya bambanta da yanayin tashin hankali da ya samu a shekarar 2022.
Tinubu ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnatin tarayya za ta ba da gudummawa don ganin an kammala aikin jirgin ƙasa na Kaduna. Yayi kira ga ragowar gwamnoni da su bi sahun gwamnan Kaduna na gina cibiyoyin kwarewa da bayar da horo.
A nasa ɓangaren, Gwamna Sani ya yaba wa shugaban ƙasa saboda goyon bayansa ga jihar. Ya ce: “Arewa ta zama ginshiƙin shirin gwamnatin tarayya na sabon fata.
Gwamnan ya ƙara da cewa: “Tinubu ya cancanci goyon bayanmu, kuma ba za mu daina yaba masa ba.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp