Shugaban kasa Bola Tinubu ya ɗage tafiyarsa zuwa birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu, da Luanda a Angola, saboda jiran bayanan tsaro kan ɗaliban da aka sace a Jihar Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada a Eruku, Jihar Kwara.
Bayan roƙon da Gwamnan Jihar Kwara ya yi, Shugaban Ƙasar ya umarci a tura ƙarin jami’an tsaro zuwa Eruku da dukkanin yankunan Ƙaramar Hukumar Ekiti.
- Majalisar Dokokin Nasarawa Ta Koka Kan Barazanar Tsaro, Ta Nemi Gwamna Ya Ɗauki Matakin Gaggawa
- Fadar Shugaban Ƙasa Ta Zargi Turaki Da Cin Amanar Nijeriya Saboda Kiran Trump Ya Kawo Wa PDP Ɗauki
Haka kuma ya umarci ’yansanda su bi diddigin ’yan bindigar da suka kai harin a cocin.
Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Tinubu ya shirya tashi daga Abuja a ranar Laraba domin halartar Taron G20 a Afrika ta Kudu sannan daga baya ya wuce Angola domin halartar taron AU-EU karo bakwai.
Sakamakon harin da aka kai a Jihar Kebbi da kuma harin da aka kai cocin Christ Apostolic Church da ke Jihar Kwara, Shugaban Ƙasa ya yanke shawarar ɗage tafiyarsa zuwa Afrika ta Kudu.
Yanzu haka yana jiran rahoto daga Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, wanda ya kai ziyarar jaje Kebbi a madadinsa, da kuma rahoton ’yansanda da Hukumar DSS kan abin da ya faru a Kwara.
Shugaban Ƙasa Tinubu ya sake umartar hukumomin tsaro da su yi duk mai yiwuwa domin ceto ɗalibai 24 da aka sace a Kebbi.














