Shugaba Bola Tinubu ya amince da sabon tsari na sayar da ɗanyen man fetur ga masana’antar cikin gida a Nijeriya, ciki har da Matatar Dangote, ta amfani da Naira maimakon kuɗin ƙasar waje. Shugaban hukumar kuɗaɗen shiga ta ƙasa (FIRS), Zacchues Adedeji ne ya sanar da hakan bayan taron majalisar zartaswa (FEC) a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
A cewarsa wannan mataki an ɗauke shi ne don rage dogaro da Nijeriya ke yi da kuɗin ƙasar waje wajen shigo da man fetur, wanda ke ɗaukar kashi 30 zuwa 40 cikin 100 na kuɗaɗen musayar.
- Duk Da Sulhu, Tsugune Ba Ta Kare Ba Tsakanin Dangote Da Mahukuntan Mai
- Tsakanin Dangote Da Mahukuntan Fetur: Ina Muka Dosa?
Adedeji ya bayyana cewa dabarar cinikayya tsakanin Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) da masana’antu na cikin gida, ciki har da babbar matatar Dangote, duk cinikayyar yanzu za a gudanar da su ne a Naira.
Ana tsammanin wannan tsari zai ceto Nijeriya kimanin dala biliyan ₦7.3b a kowace shekara ta hanyar rage nauyin kasafin kuɗin waje. Ta hanyar amfani da Naira wajen cinikayyar man fetur, gwamnati na fatan daidaita farashin ɗanyen man fetur a cikin gida da kuma rage tasirin canjin kuɗaɗen waje a kan tattalin arziƙin ƙasa.
Domin sauƙaƙa aiwatar da wannan sabon tsari, an zabi Afreximbank a matsayin bankin gudanar da hada-hadar kuɗaɗen.
Wannan canji ana sa ran zai rage matsin lamba a kan ajiyar kuɗaɗen musayar Nijeriya, tare da rage kashe kuɗaɗen musayar ƙasa daga dala miliyan ₦50m a kowane wata zuwa kimanin dala miliyan ₦600m, wanda zai taimaka wajen samar da kwanciyar hankali da bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.