Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan ya kwashe kwanaki bakwai a Saudiyya da Guinea-Bissau.
Jirgin shugaban kasa Tinubu ya sauka da misalin karfe 7:05 na daren ranar Alhamis a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
- Kotun Daukaka Kara Ta Ayyana Zaben Gwamnan Zamfara A Matsayin Bai Kammala Ba
- Gwamnatin Kano Ta Yi Kira A Kwantar Da Hankali Gabanin Hukuncin Kotun Daukaka Kara
Ya isa kasar Guinea-Bissau, inda ya halarci bikin cika shekaru 50 da samun ‘yancin kai na kasar.
Idan ba a manta ba shugaban ya Nijeriya a ranar Alhamis 9 ga watan Nuwamba domin halartar taron koli na Saudiyya da kasashen Afirka da aka gudanar a ranar 10 ga watan Nuwamba.
Shugaban ya gudanar da Umarah a ranar Lahadi a Makkah bayan kammala taro da mahukuntan Saudiyya.
Da yammacin Laraba ya bar Saudiyya zuwa birnin Bissau, inda ya halarci bikin cikar kasar Guinea Bissau shekaru 50 da samun ‘yancin kai a ranar Alhamis.