Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya gwangwaje dukkan ‘yan wasa da sauran jami’an tawagar Super Eagles da kyautar filaye da gidaje da lambar kasa ta MON saboda kwazon da suka nuna yayin gasar kofin kasashen Afirika da aka kammala a kasar Cote de’Voire.
Shugaba Tinubu wanda ministan birnin tarayya Abuja, Nysome Wike, ya wakilta yayin da tawagar Super Eagles ta ziyar ce shi a fadar shugaban kasa da ke Aso Rock Villa.
- AFCON 2023: Tinubu Zai Karɓi Baƙuncin Tawagar Super Eagles A Fadarsa Da Ke Abuja Yau Talata
- AFCON 2023: Muna Alfahari Da Yadda ‘Yan Wasan Super Eagles Suka Wakilci Nijeriya – Tinubu
Bayan wadannan kyaututtuka, an kuma yi masu alkawarin ba ‘yan wasan kyautar gida.
Shugaba Tinubu, ya yaba da kokarin da ‘yan wasan da masu horar da su suka nuna yayin gasar AFCON 2023.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp