Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya tashi daga Abuja zuwa Awka, babban birnin Jihar Anambra, domin ziyarar aiki ta kwana ɗaya.
A yayin ziyarar, zai buÉ—e wasu muhimman ayyuka d Gwamna Chukwuma Soludo ya kammala.
- Almundahana: LP Ta Nada Sanata Ireti Kingibe Domin Binciken Tsohon Shugaban Jam’iyyar
- Ko Kun San Dalilin EFCC Na Kama Gudaji Kazaure
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa Shugaba Tinubu zai ƙaddamar da Cibiyar Emeka Anyaoku ta Nazarin Harkokin Ƙasa da Diflomasiya da ke cikin Jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke Awka.
Hakazalika, zai buɗe wajen shaƙatawa na Solution Fun City wanda ya ƙunshi ƙungiyar ƙwararru da filin nishaɗi.
Bugu da ƙari, shugaban zai ƙaddamar da sabon ofishin gwamnatin jihar wato Government House Mini City, Anambra Tower of Light, da kuma wani gagarumin abin tunawa mai ɗauke da gumakan jaruman Anambra guda biyar.
Gwamna Soludo zai shirya babban taron girmamawa domin tarbi shugaban ƙasa kafin ya dawo Abuja daga bisani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp