Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya rantsar da Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
An gudanar da bikin rantsarwar ne a ranar Alhamis a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, mako guda bayan Majalisar Dattawa ta amince da nadinsa a ranar 16 ga watan Oktoba.
- Sanarwar Bayan Taron Jks: Mene Ne Sirrin Kwarin Gwiwar Kasar Sin?
- Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Waɗanda Fashewar Tankar Mai Ta Rutsa Da Su A Neja
A yayin taron, Shugaba Tinubu ya buƙaci Farfesa Amupitan da ya tabbatar am gudanar da sahihancin zaɓe a Nijeriya tare da inganta INEC domin tabbatar da gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci.
An tabbatar da naɗin Amupitan bayan Majalisar Dattawa ta tantance shi, inda ta tabbatar da cewa yana da ƙwarewa da hangen nesa wajen gudanar da ayyukan hukumar.














