Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya jaddada cewa; gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen lalubo masu son zuba hannun jari a fannin kiwo a Nijeriya.
A cewar tasa, ta hakan ne za a iya kawo karshen yawan samun rikice-rikice a tsakanin Manoma da Makiyaya a fadin kasar tare da yakar yunwa da fatara da kuma kara habaka tattalin arzikin Nijeriyabaki-daya.
- Nijeriya Ta Shirya Magance Matsalar Almajirai – Tinubu Ga Macron
- Tinubu Zai Tafi Afirka Ta Kudu Daga Faransa
Tinubu ya bayyana haka ne, a cikin sanarwar da mai ba shi shawara na musamman a fannin sadarwa da tsare-tsare; Bayo Onanuga ya fitar a birnin de Janeiro, na Kasar Brazil.
Sanarwar ta ce, shugaban ya yi wannan furuci ne a jawabinsa, bayan sanya hannu da wani kamfanin sarrafa Nama (JBS), a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil ya yi.
Kamfanin, ya kasance daya daga cikin manyan kamfanoni a duniya da ke sarrafa Nama.
A cewar tasa, abin da muka mayar da hankali yanzu a Nahiyar Afirka shi ne, lalubo mafita a kan rikice-rikicen Manoma da Makiyaya, musamman don rage asarar rayuka da dukiyoyi da kuma kara dawo da martabar kiwo.
Har ila yau, ya bukaci kamfanin ya yi amfani da wannan dama wajen sanya hannun jarin na kimanin dala biliyan 2.5, inda ya bai wa kamfanin tabbacin cewa; za a samar musu da kyakkyawan yanayi na yin kasuwanci.
Shi kuwa, Ministan Ma’aikatar Bunkasa Kiwon Dabbobi; Idi Muhktar Mahia, wanda ya jagoranci wata tawaga da Tinubu ya tura zuwa taron kafin ya isa kasar ta Brazil, a jawabin da ministan ya yi wa Tinubu ya sheda masa cewa, ya kai ziyara ga wasu manyan kamfanoni a Brazil; domin duba yadda suke gudanar da ayyukansu da kayan aiki na zamani kan sarrafa Nama.
Kamfanin na JBS S.A, na sarrafa Shanu 33,000 tare da tsintsaye sama da miliyan takwas, wanda ya sanar da cewa; yana da kyau Nijeriya ta yi hadaka da su.
Idi ya kara da cewa, kamfanin na da ma’aikata sama da 200,000 da suka fito daga sama da kasashe 50, ciki har da Kasar Amurka Kanada, Mexico da kuma Saudiya.
Haka zalika, shugaban kamfanin Wesley Batista; ya bayyana jin dadinsa kan yunkurin wannan hadaka, inda ya sanar da cewa; mun ji dadi da za mu yi aiki da Nijeriya, domin kara habaka fannin kiwon kasar.
Haka nan, Batista ya bayar da tabbacin cewa; nan ba da jimawa ba ake sa ran, kamfanin na JBS; zai fara gudanar da ayyukansa a Nijeriya.