Domin karrama goron gayyata da Mai Martaba Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya yi wa Shugaba BolaTinubu, ana sa ran zai tashi daga birnin Legas zuwa kasar Qatar a ranar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu, 2024 domin ziyarar aiki da kara karfafa alakar habaka tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.
A yayin ziyarar ta kwana biyu, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya fitar a daren Laraba, ta bayyana cewa, shugaba Tinubu zai shaida rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyin da suka mayar da hankali kan inganta tattalin arzikin Nijeriya musamman a fannonin kasuwanci, ilimi, al’adu. ma’adanai, noma, da iskar gas, tare da haɓaka haɗin gwiwa kan yaƙi da ta’addanci.
- Gwamnan Zamfara Ya Rabawa Makarantu 250 Kayan Karatu Da Fitilu Masu Amfani Da Hasken Rana A Jihar
- Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan Mutane 5, 10 Sun Jikkata A Hanyar Legas Zuwa Ibadan
Ya ce, shugaban zai kuma halarci wani taron kasuwanci da zuba jari wanda zai hada manyan jami’an gwamnati da masu zaman kansu daga Nijeriya da Qatar don kawo ci gaba a fannoni daban-daban da za su taimaka ga amfanar da juna.
Ya kara da cewa, “Shugaban zai samu rakiyar wasu manya daga cikin jami’an gwamnati a yayin ziyarar ta shaida sanya hannu kan yarjeniyoyi.”