Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin jam’iyyar APC a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Laraba.
Majiyoyi daga cikin taron sun bayyana cewa wannan ganawa na da muhimmanci wajen tsara dabaru kafin babban taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) da jam’iyyar za ta gudanar ranar Alhamis.
- Tinubu Ba Zai Taɓa Tauye ’Yancin Kafafen Yaɗa Labarai Ba, In ji Ministan Yaɗa Labarai
- Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP
Taron da aka gudanar a ƙofa a kulle ga ƴan jarida a zauren taro na fadar shugaban ƙasa ya fara tun da misalin ƙarfe 7 na yamma, inda ya haɗa dukkan gwamnonin da ke ƙarƙashin inuwar jam’iyyar, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Sanata Hope Uzodimma na jihar Imo.
Ana sa ran cewa dukkan gwamnonin APC 24 za su halarci wannan ganawa, wacce ta zo sa’o’i kaɗan kafin babban taron NEC da za a yi da karfe 2 na rana a Banquet Hall na fadar shugaban ƙasa ranar Alhamis, 24 ga Yuli, 2025.
Daga cikin batutuwan da za a tattauna akwai maye gurbin shugaban jam’iyya na ƙasa, bayan murabus da Dr. Abdullahi Ganduje ya yi. Ana ganin wannan taron NEC na iya zama muhimmin mataki wajen dawo da daidaito a cikin jam’iyyar, musamman kafin zaɓuɓɓukan ƙasa da na jihohi da ke tafe a 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp