A ranar Talata ne wani jirgin kasa da ya taso daga tashar Kubwa da ke Abuja zuwa Kaduna ya kauce hanya, mintuna kadan da tashinsa, inda fasinjoji akalla 14 suka jikkata, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin matafiyan.
Tuni dai, Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Kasa ta Nijeriya (NRC), ta sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragen; har zuwa wani lokaci.
- Me Ya Sa Wasu Kafofin Watsa Labarun Japan Suke Kokarin Musanta Kisan Kiyashin Nanjing?
- Manyan Jami’ai A Ma’aikatar Tsaro Ta Cikin Gida Za Su Ci Gaba Da Karɓar Albashi Har Ƙarshen Rayuwa
LEADERSHIP, ta tattaro cewa; jirgin wanda ya kunshi tarago guda 10, ya taso ne daga kadan bayan karshe 11 na safe daga Kubwa.
Har ila yau, hukumar jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana cewa; an fara bincike kan hatsarin da jirgin kasan daga Abuja zuwa Kaduna ya yi a garin Asham da ke Jihar Kaduna.
Hukumar ta ce, binciken zai gudana ne karkashin kulawar hukumomin da abin ya shafa tare da sa ido daga ma’aikatar sufuri ta tarayya, domin kokarin gano musabbabin faruwar al’amarin.
A cikin sanarwar da NRC ta fitar a yammacin ranar Talata, ta bayyana cewa; jimillar mutum 618 ne suke cikin jirgin a lokacin da ya sauka daga kan hanyarsa.
Kazalika, hukumar ta bayyana cewa; daga cikin fasinjojin, mutum akalla 14 ne suka samu raunuka daban-daban, sannan kuma an garzaya da su asibiti. Sauran fasinjojin kuma, an mayar da su zuwa tashoshin Idu da Kubwa cikin wani jirgi da aka turo daga Abuja.
Haka kuma, an dakatar da dukkanin ayyuka da zirga-zirgar jirgin kasan daga Abuja zuwa Kaduna na dan wani lokaci, har sai an kammala bincike da kuma gyara hanyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp