Shugaban ƙasa Bola Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗi na shekara ta 2025 ga taron majalisar dokokin ƙasa a ranar Talata, 17 ga Disamba, 2024. Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio, a yayin zaman majalisar yau Alhamis.
“Shugaban ƙasa ya sanar da majalisar dokoki niyyarsa ta gabatar da kasafin kuɗi na 2025 a taron haɗin gwuiwar majalisu a ranar 17 ga Disamba, 2024,” inji Akpabio.
Kasafin kuɗin da aka gabatar na N47.9 trillion an bayyana shi ne daga bakin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu.