Shugaba Bola Tinubu, zai bar Abuja babban birnin tarayya, a yau Lahadi zuwa Legas don yin bikin karamar sallah.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar ranar Asabar.
- Karin Kudin Hajji: Gwamna Inuwa Ya Tallafa Wa Maniyyatan Gombe Da Naira 500,000 Kowanne
- Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Gana Da Sakatariyar Baitulmalin Amurka A Guangzhou
“Shugaba Tinubu zai yi bikin sallah ne tare da iyalansa a Legas, inda zai yi amfani da lokacin wajen yi wa Nijeriya addu’a, musamman ganin irin tarin matsaloli da kasar ke fama da su,” in ji sanarwar.
“Kuma zai ci gaba da gudanar da ayyukansa kamar yadda ya saba a can,” in ji sanarwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp