Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar aiki jihar Borno ranar Asabar domin ƙaddamar da wasu manyan ayyuka da Gwamna Babagana Umara Zulum ya aiwatar. Ziyarar za ta gudana ne a Maiduguri, babban birnin jihar, a cewar sanarwar gwamnatin jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Borno, Farfesa Usman Tar, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a. Ya ce Shugaban Ƙasa zai zo ne domin ƙaddamar da muhimman aiyukan raya ƙasa da gwamnatin Zulum ta aiwatar a fannonin ci gaba daban-daban.
- Sojoji Sun Yi Kuskuren Kashe Mutanen Gari A Borno
- ’Yan Majalisa Sun Roƙi Tinubu Ya Sake Duba Lamarin Janye Musu ’Yansanda
A cikin sanarwar, gwamnatin jihar ta bayyana maraba da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu GCFR, inda ta ce al’ummar Borno na farin cikin karɓar Shugaban Ƙasa a wannan ziyara ta aiki da za ta gudana ranar 20 ga Disamba, 2025.
Gwamnatin jihar ta yi kira ga al’umma da su fito ƙwarai domin tarbar Shugaban Ƙasa, tare da nuna ladabi, tsari da kyakkyawan hali a lokacin ziyarar. An kuma bukaci jama’a da su kiyaye doka da oda domin gudun duk wani cikas.
“Mu nuna Borno a matsayin Gidan Zaman Lafiya, doka da oda,” in ji sanarwar, yayin da ake sa ran ziyarar za ta ƙara jaddada goyon bayan gwamnatin tarayya ga ayyukan ci gaba da ake aiwatarwa a jihar.













