Abba Ibrahim Wada" />

Tottenham Za Ta Iya Korar Pochettino

Lissafi ya cigaba da dame wa Tottenham bayan da bakinta, ‘yan Bayern Munich suka kunyata ta da ci 7-0 a gasar Zakarun Turai ta Champions League saboda a wasan na Talata da daddare, girma-girma Tottenham ta fara wasan da kuzari har Son Heung-Min ya fara ci mata kwallo a minti na 12.

Bayan nan ne kuma fa sai wasa ya sauya salo minti uku tsakani murna ta koma ciki Joshua Kimmich, ya farke wa Bayern Munchen sannan kuma ana dab da tafiya hutun rabin lokaci ne kuma sai Robert Lewandowski ya kwarara wa mai tsaron ragar Tottenham, Hugo Lloris, wata kwallo daga tazarar yadi 20, ba ta zame ko ina ba sai a raga.

Dawowa daga hutun rabin lokaci ne kuma sai lissafi ya kara cabewa Tottenham, inda Serge Gnabry ya rika zura musu kwallo a raga a jere a jere a minti na 53 da na 55, wato minti biyu tsakani ya jefa kwallo biyu.

Daga nan sai Harry Kane ya dan lasa wa Tottenham a minti na 61 amma da bugun fanareti, ta samu ta biyunta kuma ta karshe kenan sai dai wasa ya yi nisa a minti na an kusa tashi a minti na 83 da kuma na 88, Gnabry ya sake zura kwallo ta shida da kuma ta bakwai.

Wannan ciye-ciye da tsohon dan wasan na Arsenal , Gnabry ya yi, ya zama dan wasa na farko a tarihin gasar ta Zakarun Turai da ya ci kwallo hudu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci kuma  a tarihi ba wata kungiyar kwallon kafa ta Ingila da aka taba ci da yawa haka a gida a duk wata gasar Turai har ila yau wannan kuma shi ne karon farko a tarihin kungiyar Tottenham na shekara 137 da kafawa da a ka ci ta kwallo bakwai a gida a duk wata gasa.

Yanzu dai ana ganin an shiga wani lokaci da kungiyar za ta sake nazarin zama da kociyanta Mauricio Pochettino, ganin irin halin kunyata da take kara shiga a bana kuma a wasannin kungiyoyin biyu na gaba Tottenham za ta ziyarci Brighton a gasar firimiya ranar Asabar da rana  ita kuwa Bayern Munich da ke ta daya a gasar Bundesliga ta Jamus za ta kasance ne a gida da Hoffenheim a ranar Asabar din.

Exit mobile version