Hauhawar farashin kayyakin masarufi da na sauran harkokin rayuwa sun kai fiye da kashi 100, wanda ba a taba samun irin haka ba a cikin shekara 10 da suka wuce, a halin yanzu ‘yan Nijeriya na sayen kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje da tsadar gaske saboda yadda kudaden kasashen wajen suka yi tashin gwaron zabi ga shi kuma hanyoyin shigan kudaden al’umma ya matukar karanta saboda matsalar tattalin arzikin da ake fuskanta a Nijeriya dama duniya gaba daya.
A yayin da hauhawar farashin ke cigaba dandana wa ‘yan Nijeriya aya a hannu, talaka da masu karamin karfi wadanda su suka fi yawa a halin yanzu sun karkata ne zuwa amfani kayayyaki masu arha musamman ganin yadda hanyoyin samun kudaden ke kara karanta.
- Wang Wenbin: Hannuwan ‘Yan Siyasar Amurka Da “‘Yan Ina Da Yaki” Na Jike Da Jinin Al’ummun Gabas Ta Tsakiya
- Dangantakar Kasar Sin Da Taiwan, Tamkar Ta Uba Ne Da Dansa
Hauhawar farashi yana faruwa ne yayin da kayayyaki suka yi tsada na wani tsawon lokaci kuma kudaden da ke a hannun al’umma ya karanta, Hukumar kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa, ana samun hauhawar farashi na fiye da kashi 18.60 ya kuma yi kamari ne a watan Yuni na wannan shekarar na 2022 wannan karin shi ne mafi girma da aka samu a cikin shekara 5 da suka wuce.
Binciken kwakwaf da jaridar LEADERSHIP ta gudanar ya nuna cewa, harkokin tafiyar da iyali na abubuwan da ke bukata na yau da kullum ya zame wani abin damuwa ga iyalai da daidaikun mutane a sassan kasar nan.
‘Yan Nijeriya na cigaba da neman hanyoyi na musamman da za su fuskanci tsadar kayayyakin masarufi da suka nakasa kudaden shigar al’umma, masana sun bayyana cewa, mutane na cigaba da kokarin sabawa tare da jure halin da ake ciki ta hanyar janyewa daga hulda da kayayyaki masu tsada zuwa kayyakin da farashin su yake da sauki don ya dace da irin kudaden da ke shigo musu.
A cewar wani masanin harkokin kasuwanci mai suna, Joseph Liadi, yayin da babu issasun kudade a hannun masu sayen kaya yakan zama dole su lura da abin da ya fi musu muhimmanci cikin abubuwan da suke bukata wanda ya yi daidai da zurfin aljihunsu.
Da yake gaskaya wannan ra’ayi da muka kawo muku a sama na yadda matsalar tattalin arzikin kasa yake takura wa kudaden shigar al’umma, wata ma’aikaciyar gwamnati, mai suna, Abigail Michael-Paul, ta bayyana cewa, saboda yadda aka samu hauhawar farashin kayan masarufi da sauran harkokin rayuwa ta kan rungumi daukar abubuwan da suka fi muhimmanci gare ta ne ba wai sayen komai mutum yake sha’awa ba.
‘Dole mu kaurace wa tare da yin takatsantsan wajen amfani da abubuwan amfanina yau da kullum kamar su, man gashi, man shafawa don su kara dadewa a gida.
“Wannan hauhawar farashin da ake fuskanta ya sanya ni dole in yi tsimin kudaden da yake shigio mini. Motar haya nake amfani da shi wajen zirga-zirga na kan kuma taka sayyada ko in hau achaba a kullum. Saboda faduwa darajar Naira da kuma hauhawar farashi, in har ina da bukatar sake wayar hannu kuma sayen wani kayan wuta na gida nakan sayi, na hannu ne wadanda ake shigo da su daga Birtaniya. Na kuma canza tsarin amfani da data na intanet a halin yanzu, nakan nemi tsarin da ya fi sauki ne wanda ya yi daidai da aljihuna.”
‘Yan Nijeriya Sun Koma Amfani Da Kayayyaki Masu Arha Wani mazaunin Abuja mai suna Malik Abdullahi, ya yi bayanin cewa, “Saboda hauhawar farshin kayayyaki na rage abubuwan da nake siya, na rage abubuwn da nake saye don ajiyewa a gida na komawa kayayyaki masu arha koda kuwa basu da inganci.
“Hauhawar farashi ya shafi kusan dukkan al’amurran rayuwa a Nijeriya, tun daga katin waya, kudin shiga mota, kudaden makarantar yara da na takardu, kusan komai ya tashi, kwanaki sai da canza wa yara na makaranta saboda na kasa daukar nauyin kudin da makarantar suka kara,’’ in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa, farashin kayayyakin abinci ya yi tashin gwauron zabi.
“Farashin buhun shinkafa ya tashi daga N12,000 zuwa N28,000, katan din kaji ya tashi daga N12,000 zuwa N20,000, yayin da buhun barkono ya tashi daga N15,000 zuwa N22,000. Banbancin farashi na taimaka nama wajen zabi a tsakanin kayayyakin da suke da tsafar da kuma wadanda suke da sauki,’’ in ji shi.
Haka kuma wani magini mai suna Joshua Gata, ya ce, hauhawar farashi ya matukar shafar kayayyakin gine-gine.
Ya kuma kara da cewa, ‘‘Buhun siminti da ake saya a N2,600 ya tashi zuwa N3,900 a cikin shekara 2 kachal.”
Wani ma’aikacin kamfani, mai suna Samuel Udoh, ya bayyana cewa, a halin yanzu yakan sayi abubuwan da yafi bukata ne kawai tare da kuma yin tsansteni wajen sarrafa kayayyakin da ya saya don kaucewa allubazaranci. Wata matar aure kuwa mai suna Misis Abiola Ojo, mazauniyar Mokola, Ibadan, a jihar Oyo ta ce, hauhawar farashin yana takutra wa rayuwa, a halin yanzu ta samu fahintar iyalanta inda suka sake salon yadda suke amfani da kayayyakin masarufi, abubuwan da suke na alfarma da a halin yanzu an kawar da su don fuskantar halin da ake ciki na hakika. Haka kuma wani Direba mai suna Aliyu Musa, wanda ra’ayinsu daya, ya ce, “Ba zan kashe kai na ba, zan sayi abin da zan iya ne kawai,”.
Wani masanin harkokin kudade mai suna Ebuka Chukwu, ya ce cikin hanyoyi da dabarun fuskantar tsadar kayayyakin abinci shi ne cin abinci a gida.
Ya kara da cewa, “Cin abinci a waje nada matukar tsada. Yawanci kudin abincin da ake saya a gidajen sayar da abinci yana iya ciyar da iyalan ka gaba daya a gida. Duk wani da ya yi hulda da kasuwannin a ‘yan tsakanin nan zai iya tabbatar da yadda kayayyaki suka yi tashin gwauron zabi, abin ba za a iya hadawa da irin albashin da ma’aikata ke karba ba da kuma irin kudaden da ke shigowa a hannun al’umma.
“Biredin da yake cikin abinci mafi sauki a Nijeriya a halin yanzu ya yi tsadar da a halin yanzu ya fi karfin masu mu’amala da shi a baya. Kudaden mota ya yi matukar tashi, kudin jigin sama ya yi tashin gwauron zabi a halinh yanzu ana canjin fiye da N100,000 a falle daya na zirga-zirga a cikin gida, tafiya kuma a kan hanyoyin Nijeriya da ya kamata a komawa ya zama tashin hankali saboda ‘yan ta’adda masu garkiuwa da mutane ga kuma tsada’’.
Wata mata data nemi mu sakaya sunanta ta ce, tuni ta tura yaranta biyu zuwa wajen kakannin su don ta ta tabbatar da kakkannin ba za su bar su da yunwa ba, ta kuma yi hakan ne saboda halin matsi da suke fuskanta.
Wani malamin jami’a kuwa, mai suna Timi Olubiyi (Ph.D.), ya ce, annobar korona da karayar tattalin arzikin da ake fuskanta ya matukar shafar harkokin kasuwancin al’unmma da na masana’antu da kuma yadda al’umma ke gudanar da harkokin rayuwarsu a ‘yan tsakanin nan.
‘‘Babbar makasudin fada wa cikin wannan matsalar kuwa shi ne karayar tattalkin arziukin da ke fuskanta a Nijeriya wanda hakan ya shafi kusan dukkan harkokin rayuwar al’umma. Nijeriya na daga cikin kasashen da hauhawar farashi ya yi wa katutu ya kuma shafi harkokin kasuwanci da na tafiyar da gwamnati musamman ganin yadda cutar korona ta nakasa bangarori da dama na rayuwar al’umma.
Bincike ya nuna cewa, yanayin hauhawar farashi a Nijeriya a cikin shekara 61 da suka wuce, ya kasance kamar haka, -3.7% da 72.8%. a shekarar 2021, in aka hada da kashi 17.0%. za a fahinci cewa, a tsakanin shekarar 1960 zuwa 2021, ana samun karuwar farashi da kashi 16.1 cikin dari a duk shekara.
Gaba daya an samu karin kashi 566,918.02 %. Abin da ake sayarwa N100 a shekarar 1960 an sayar da shi a kan N567,018.02 a farkon shekarar 2022.
Rahoton Jaridar LEADERSHIP ya nuna cewa, babu wata kasa da ta tsira daga hauhawar farashi a duniya. A wasu sassan duniya musanmman Amurka da Birtaniya an fuskanci hauhawar farashi, tabbas an fuskanci hauhawar farashi a sasan duniya a cikin shekara 2 da suka wuce. Masana sun kuma kara da cewa, hauhawar farashi na daya daga cikin manyan matsaloloin da tattalin arzikin kasa ke fuskanta a ‘yan shekarun nan.
Hauhawar farashi a Nijeriya ya yi tashin aa ba a gani ba a cikin wata 11, a watan Mayu 2022, inda ya kai kashi 17.71 a cikin dari wanda hakan ke nuna yadda farashin ya tashi a cikin wata hudu inda farashin kayan abinci da na kayan masaufi suka fi kowanne tashi.
Wani masanin tattalin arziki mai suna, Femi Alayande, ya bayyan a wa LEADERSHIP cewa, yanayin hauhawar farashi da ake fuskanta a Nijeriya yana zuwa a daidai yadda lamarin yake a sassan duniya, musamman ganin irin rikice-rikicen da ake fuskanta a sasan duniya na yake-yake wanda ya haifar da hauhawar farashin kudin man fetur da na kayan abinci.
“Hauhawar farashi na kashe tattalin arzikin Nijeriya, ya kuma kamata a ceto ‘yan Nijeriya tare da ceto tattalin arzikin Nijeriya daga durkushewa. Ya kuma kara bayyana cewa, ‘yan Nijeriya za su cigaba da biyan kudade masu yawa don sayen kayayyakin da aka shigo da su daga kasashen waje saboda yadda Naira ta fadi warwas, kudin ruwa a bankuna za su kuma cigaba da tashi haka kudaden makaranta na yaran da suke karatu a kasashen waje zai cigaba da karuwa, tuni dai ake fuskantar tsakar kayayyakin abinci, kudaden mota da sauran na harkokin yau da kullum, farashin man fetur yana ta tashin gwauron zabi, tabbass harkokin rayuwa a ‘yan shekaru masu zuwa abu ne da sai an yu taka tsantsan, Allah ya taimake mu.