A yayin da ake ci gaba da fuskantar matsralar tsadar rayuwa, ‘yan NIjeriya na kashe kudaden su wajen ciyar da kansu da iyalansu ba tare da sanin yaushe za a samu sauki ba. Wananna ne kuma ke tura al’umma fadawa cin bashi ta kowannne hali, masana sun kuma nuna cewa, bashi na kara jefa al’umma cikin halin masti da tashin hannkali, sai dai kuma wasu da aka tattauna da su sun yi fatan al’amurra su daidaita nan da wata 6 masu zuwa.
Wani binciken jin ra’ayi na Babban Banki Nijeriya CBN ya yi a watan Yuli wanda ake kokarin jin abin da al’umma ke fata a duk wata, a jin ra’ayin da aka yi na watan Yuli, al’umma sun yi fatan samun sauki a sauran watanni 6 da suka rage na shekarar 2024. Sun ce tsadar rayuwa ya jefa su fadawa cin bashi domin toshe matsalar da suke fuskanta na rayuwa. Ko
- Darajar Naira: Tsohon Dan Majalisa Da Ya Ci Bashin Karatu N1,200 A Shekaru 47, Yanzu Ya Biya Da Fiye Da Naira Miliyan 3
- An Cafke Wani Hedimasta Bisa Laifin Sayar Da Kayayyakin Makaranta A Kano
An gudanar da binciken ne a tsakanin ranakun 22 zuwa 26 na watan Yuli 2024, inda kashi 99.7 na wadanda aka ba takardar tambayoyin suka bayyana cewa, suna sa ran karuwar tsadar kayayyaki a kasuwanni.
Al’ummar da aka tataunawa da su sun ce, wannan ba lokaci ne na sayen wasu manyan kayayyaki ba kamar motoci gidaje da filaye, sun kuma nuna fatan karyewar naira a kasuwanin kudaden kasashen waje, sun ce za a kuma samu karuwar ruwan bashi na banki da karuwar rashin aikin yi a tsakanin matasa.
Sun ce, za a samu karayar tattalin arziki in har farashin kayayyaki ya ci gaba da tashi, da yawa kuma na bukatar ganin an samu raguwar ruwan da ake dorawa bashi domin masu kanana da matsaikaitun masana’antu.