- Babbar sallah a wannan shekarar ta zo a cikin wani yanayi na tsadar rayuwa bisa yadda farashin kayan masarufi suka yi tashin gwauron zabi inda hakan ya shafi ragunan da ake layya da su.
Wakilanmu a sassan Nijeriya musamman yankin arewa, sun duba yadda magidanta ke kokarin sama wa kansu mafita game da yadda za su gabatar da bikin babbar sallar.
A yayin da was uke kokarin sun sayi ko da karamin rago ne da ake ce wa “ka fi zuru”, wasu kuwa cewa suka yi sun hakura, idan makwabta sun yi, sai su ba su sadaka.
- Za A Yi Sallah Babu Lantarki A Jahohin Kano, Jigawa, Katsina, Ma’aikatan KEDCO Sun Shiga Yajin Aiki
- ‘Yansanda Sun Hana Hawan Sallah A Kano
Wani magidanci da aka zanta da shi a Kaduna, Yusuf Ibrahim ya ce, tun yana gwauronsa yake yin layya, amma bana saboda tsadarsu, bai ma sa aka ba; domin gwanda ya sayi kayan abinci da ya sayi Rago a kan Naira 150,000 ko sama da haka, a cewarsa, “na jira wadanda suka yi layyar su ba ni na sadaka.”
Shi ma Abubakar Yahaya Amale cewa ya yi, “Ina yin layya duk shekara, amma bana na hakura; na ji kanshin suya a makwabata, domin rayuwa ta yi tsanani kwarai da gaske, yanzu da sayen Rago zan ji ko da tsadar kayan masarufi, sai a nuna maka dan makyazon Rago ana ce da kai Naira 150,000.”
“Raguna sun yi tsada matuka, sai ka ga dan karamin Rago ana ce maka Naira 150,000 zuwa sama, sai ka ce mutum zai biya kudin gidan haya. Ba a taba samun shekarar da farashin Raguna ya yi tashin gwaron zabi kamar bana ba, domin na ga Ragon da farashinsa ya kai Naira 500,000 da na Naira 700,000, har da na Naira 900,000, sai ka ce mutum zai sayi Mota. Kamar yadda Alhaji Mustapha Ahmad Tijjani da Alhaji Abdullahi Barazana suka bayyana.
A tattaunawarsa da LEADADERHIP Hausa, wani babban dila a bangaren sayar da Raguna a gafen titin Unguwar Hayin Malam Bello a Kaduna, Ishak Aliyu Babayo ya ce; farashin raguna a bana, abin sai dai kawai addu’a. “Manyan muna sayar da su daga Naira 300,00 zuwa 350,000 a bana, wadanda a bara farashinsu, bai wuce daga Naira 150,000 zuwa sama ba, ya danganta da girmansa. Mun sayar wasu kananan a bara daga Naira 70,000 zuwa Naira 80,000, amma a bana farashin nasu ya yi matukar tashi.
“Hatta kudaden da muke jigilarsu zuwa cikin Kaduna daga jihohin da muke sayowa, ya rubanya, domin a bara muna jigilarsu a manyan motoci daga Naira 200,000 zuwa Naira 250,000, amma a bana muna biyan daga Naira 400,000 zuwa sama, ya danganta da nisan garin da muka sayo su,” in ji shi.
Har ila yau, “Farashin abincinsu ya karu; misali Kowar Farin Wake a bara ana sayar da ita kan Naira 3,500, amma a bana ta kai Naira 10,000 zuwa 11,500”.
Ya ci gaba da cewa, ana sayar da Kaikayin Dawa a bara kan Naira 2,500, amma a bana ya kai Naira 7,500, inda kuma buhun Dusa a bara ake sayar da shi kan Naira 5,000, a bana kuma ya kai Naira 7,500 ko sama da haka.
Binciken da wakilinmu ya yi a fitacciyar kasuwar nan ta sayar da dabbobi da ke Tudun Wada Kaduna, ya gano yadda ake samun karancin masu zuwa kasuwar, don sayen wadannan Raguna a bana.
Wani babban dila a ksuwar, Alhaji Kabir Sani ya danganta tashin farashin, musamman na Rugunan a kan kalubalen rashin tsaro, musamman a Jihar Zamfara; inda nan ne mafi akasari suke zuwa domin kawo dabbobin.
A cewarsa, akwai kuma manya wadanda duk guda daya ya kai daga Naira 800,000 zuwa Naira miliyan 1.4, wanda farashin daya a bara, bai wuce Naira 500,000 ba, duk da cewa ko shakka babu; wannan na da alaka da tashin farashin kayan masarufi da kuma matsin tattalin arziki da ake fama da shi a wannan kasa.
Haka nan, a Kasuwar Kawo; wani dilan sayar da Raguna a gefen hanyar titin Waff duk dai a Kadunan, Awwal Mohammed ya ce; farashin Rago daya da ake sayarwa kan Naira 200,00 a bara, bana ya kai Naira 400,000, matsakaici kuma a bana ya kai Naira 300,000, inda muke sayar dan karami kuma a kan kudi daga Naira 100,000 zuwa Naira 150,000 ko sama da haka, ya danganta da girma Ragon.
Kebbi
Jihar Kebbi na daya daga cikin Jihohin Arewa Maso Yamma da aka san su da kiwon dabbobi da kuma noma. A duk shekarar Sallar layya, musamman lokacin da dabbobi na araha; mutane daga sassan kasar daban-daban na aiko da kuddensu a saya musu dabbobin da za su yi layya, misali kamar Jihar Legas, Abuja, Kaduna da sauran makamantansu.
Amma abin takaici, a bana mutane daga kowane bangare na kasar nan, kokawa suke yi kan wannan tsada ta dabbobi; wadda ba a taba ganin irin ta ba.
Wakilinmu ya yi tattaki zuwa kasuwar dabbobi da ke babban birnin jihar, wato Birnin Kebbi; domin ganin irin wainar da ake toyawa a kasuwannin wannan dabbobi. Inda ya yi kicibis da wani magidanci mai suna Suleiman Dan-Binta, wanda ya shigo kasuwar da nufin sayen rago.
“Innalillahi wa inna’lailhi raju’un! Magana ta gaskiya, ba kowa ne zai iya sayen dabbar layya bana ba, dalili kuwa shi ne dabbobi sun yi tsadar da ba mu taba ganin irin ta ba a wannan jiha”, in ji shi.
“Na zo da Naira 150,000, don sayen Raguna guda biyu; amma na lura cewa, Rago daya kacal kudin zai iya saya min, kuma ko guda dayan ma karami ne. A shekarar da ta gabata, Raguna biyu na saya a kan kudi Naira 135,000, amma fa a yau Rago daya ne ake maganar 150,000; ka ga hakan wata matsala ce da ta kunno kai a cikin al’ummarmu, wanda jama’a da dama na fama da tsadar rayuwa da kuma talauci, sannan kuma ga rashin wadataccen abinci da kuma tsadarsa.
Shi ma Manu Alhaji da ke Uguwar Bayan Kara cikin babban birnin jihar ya bayyana cewa, “Na shigo wannan kasuwa ne da Naira 110,000 da nufin sayen dabbobin layya, amma na yanzu na tabbatar da cewa; ba zan iya sayen dabbar layya a wannan shekara ba, domin kuwa na ga dabbobin sun yi matukar tsada; wadda ta saba wa hankali. Wannan dalili ne ya sa na yanke shawarar komawa gida da ‘yan kudadena, na bai wa iyalaina hakuri cewa; ba zan iya yin layya a bana ba”, a cewar Alhaji.
Har ilayau, wani dan kasuwa, Bagudu Dan-Zabarma ya yi bayani a kan yanayin yadda kasuwar dabbobin ke tafiya, inda ya bayyana cewa, “Kasuwar dabbobi a wannan shekara, sai dai kawai hakuri, domin kuwa dabbobin sun yi matukar tsada; sannan kuma ga karancin masu saya sakamakon rashin kudi da faman da ake yi na matsin rayuwa a tsakanin wannan al’umma.” In ji shi
Katsina
Kamar kowace shekara, a bana ma masu kiwon dabbobi da sayen Raguna su sayar a matsayin kasuwanci, sun shiga tsaka mai wuya a Katsina; sakamakon yadda mutane suka yanke tsammani a kan sayen Raguna.
Daga cikin wasu kasuwannin wucin gadi da ake kafawa a cikin birnin Katsina, alamu sun nuna cewa; kasuwannin na neman ba su ruwa, sakamakon yadda dabbobin suka yi tsada; mutane kuma ya kasance babu kudi a hannunsu.
Haka zalika, wasu na bayyana cewa; an zo wani lokaci da mutane yanzu ba ta layya suke ba, batun abinci ne kadai a gabansu; amma idan Allah ya ba da iko, sai a hada duka biyun.
Binciken da LEADERSHIP Hausa ta yi a cikin birnin Katsina ta gano cewa, an kara samun yawan kasuwannin wucin gadi a cikin birnin na Katsina; duk da cewa babu ciniki a wannan shekara.
Har ila yau, akwai ire-iren wadannan kasuwanni a kusa da gidan Amadi Kurfi, kan titin IBB da kusa da Masallacin Bani Kumasi da kusa da ofishin Hukumar Alhazai ta Jihar Katsina da kuma kasuwar ‘yar Kutungu.
Sannan, akwai masu sayar da wadannan dabbobi da dama a kan hanya, inda wani ya bayyana cewa; lallai akwai matsalar ciniki a wannan shekara.
Wasu kuma sun bayyana cewa, duk da wadannan matsaloli da ake da su, ana samu ana sayarwa a kadan-kadan; amma dai kasuwar ta zama sai a hankali.
Wata hajiya, Ambasada Khadija Sulaiman Saulawa da wakilinmu ya zanta da ita, ta bayyana cewa, ta je kasuwa da kudinta; kimanin Naira 85,000, amma sai dawowa ta yi da kudin saboda tsada.
Saulawa ta kara da cewa, za ta ajiye kudinta har zuwa ranar Sallah; idan ta samu ciko ko kuma mai sauki, sai ta yi layyar; idan kuma ba ta samu ba, ta hakura.
Wani bincike ya tabbatar da cewa, yanzu magidanta da dama sun yanke shawarar yin abinci maimakon yin wannan layya, sakamakon yadda dabbobin suka yi matukar tsada.
Kano
Kowace shekara, Babbar Sallah na da nata irin salon da take zuwa da shi; amma wannan shekarar nata salon na daban ne, sakamakon yadda al’ummar musulmi suka tsinci kansu a wani irin yanayi na matsin tattalin arziki da kuma tsadar rayuwa.
Kasuwannin sayar dabbobi a Kano, sun kasu kashi uku; da farko akwai kasuwannin kauye, wanda daga nan ake kawo mafi yawan dabbobin da ake sayarwa a irin wannan lokaci na gabatowar Sallah, sai kuma kasuwannin tafi da gidanka; inda ake ganin wasu rukunin mutane na janye da raguna suna zagawa da su unguwannin masu hannu da shuni, sai kuma kasuwannin da ake da su na asali irin su ‘Yan Awaki, Abba Tuwa, Unguwa uku da sauran makamantansu.
Wadannan kasuwanni dukkanninsu sun yi carko-carkoi babu ciniki, amma duk da haka za ka tarar da mutane ‘yan kalilan da suke iya lekawa, don jin farashin dabbobin.
A Kasuwar Gomo, wata Kasuwa da ke da iyaka da Dajin Falgore; a yankin Karamar Hukumar Sumaila, a nan ne ake kyautata zaton samun saukin wadannan dabbobi, kasancewar Fulani na fitowa daga fitowa daga wannan daji; don sayar da dabbobi.
Wani dillalin dabbobi, Muhammadu mai Tirke ya bayyana wa wakilinmu cewa, an kawo wata Tinkiya guda daya da aka taya kan Naira 180,000, amma a shekara ukun baya da suka wuce; Tinkiya kamar wannan ba ta wuce Naira 17,000 zuwa 20,000 ba.
“Haka nan, da shekara ta sake zagayowa; mun sayar da Raguna masu tashen koshi a kan Naira 40,000 zuwa 55,000, amma a wannan shekarar; ana sayar da dan timbirbirin Rago a kan Naira 100,000, maganar da ake yi a halin yanzu ga wani can an taya shi a kan Naira 600,000; an ki sallamawa”, in ji mai Tirke.
Ita kuma Kasuwar dabbobi ta unguwa uku, wadda ‘yan birni ke yayin ta, farashin Raguna na farawa ne daga Naira 200,000 zuwa abin da ya yi sama, hakan ya sa dillalai da masu fataucin dabbobin yin tagumi.
Da aka tambayi Sarkin Tirke kan ko mene ne dalilin wannan tsadar da dabbobi a daidai wannan lokaci, sai ya amsa da cewa; “Wallahi wanda duk zai ce maka ga hakikanin dalili, sai dai ya yi shaci-fadi. Domin dai ka ga yadda yanzu man fetur ya samu, ita ma kuma dalar an ce ta yi kasa, amma farashin dabbobi kullum kara sama yake yi; amma mu a namu zaton, kawai wata jarrabawa ce daga Allah da take bukatar tsanannata addu’a.”
Shi kuwa Alhaji Dan’asabe, wani dillalin dabobi shi ma a Kasuwar dabbobi ta ‘Yarkasuwa cewa ya yi, “Wannan ba abin mamaki ba ne a wurinmu; domin dama mun yi zaton haka, tun lokacin da aka bayyana tashin kudin kujerar Hajji; ta koma kusan Naira miliyan takwas”, in ji shi.
Saboda haka, yanzu a Kano dai kallo ya koma sama, domin kuwa talakwa da dama sun mayar da hankali wajen cigiyar wuraren da ake rabon naman sadaka, irin wanda wasu kungiyoyi daga kasashen waje ke kawowa ciki har da mutanen Turkiyya da sauran makamantansu.
Koda-yake, a gabatowar wannan babbar Sallah; an ce akwai wata kungiya da ta tsara yin rabon Shanu kimanin 2,000, don tallafa wa talakawa, hakan tasa mutane suka bazama; domin gudun ka da su ma a yi babu su.
Bauchi
Babu shakka, a Jihar Bauchi Raguna sun yi matukar sauki ba kamar yadda abin yake a wasu jihohi ba, Shanu kadai dai suka yi tsada kawarai da gaske; duk da cewa, wakilinmu ya yi kokarin gano batun tsadar Shanun; da yawan bukatar da ake yi musu fiye da Raguna a jihar.
A zantawarsa da LEADERSHIP Hausa, Malam Abubakar Isa daga babbar kasuwar Shanu ta Bauchi, ya yi cikakken bayani dangane da wannan tsada da dabbobi suka yi.
Har ila yau ya yi nuni da cewa, masu yin kutse a wannan sana’a ta dabbobi a dare daya; su ne ke jawo tsadar dabbobin, domin kuwa da yawansu suna shiga kasuwancin ne, don samun riba fiye da kima; sannan mafi yawancinsu suna sayo dabbobin ne da tsada daga kasuwannin kauyuka, saboda ba sana’arsu ba ce.
“Muna da rukunin kananan Raguna daga Naira 60,000, 80,000 har zuwa 100,000, wadanda ‘yan madaidaita. Sai kuma na Naira 110,000, 150,000 ‘yan tsaka-tsaki, sannan kuma akwai manya daga Naira 160,000 zuwa 200,000, akwai kuma manya da suka kai har zuwa Naira 400,000.”
Ya bayyana cewa, a da ana shigo da Raguna daga wurare daban-daban, amma yanzu manyan hanyoyin samun su a Jihar Bauchi, su ne kauyukan jihar.
“Ana shigo da Raguna daga yankunan Azare, Soro, Dambam, Alkaleri, Gadan Maiwa, Maraban Liman Katagum da sauransu. Mutanen wannan gari na Bauchi su ne ke kiwata wadannan Raguna, su kawo kasuwa su sayar; duk da cewa akwai wadanda ake sayowa daga waje, amma mafi yawansu wadanda mutane suka kiwata da kansu ne. Bayan sun sayar da manyan da suka kiwata, sai kuma su sayi kanana su sake girkewa har sai kuma wata shekara”.
Haka zalika, “Batu na gaskiya, raguna na da sauki a Bauchi, domin hatta su kansu masu sayen idan sun zo suna fada mana cewa, akwai bambancin farashi a wannan kasuwa tamu, idan aka kwatanta da sauran wasu wurare da suka fara bincikawa kafin su zo nan.
“Mu saboda yau da gobe, muna cikin wannan sana’a; mun fi wadanda suke shigowa da tsakar rana samun sauki. Sabbin shiga sana’ar, wadanda suke sayarwa a cikin gari su ne za ka ji suna kiran kudin Ragunan fiye da hankali, saboda ba su san kan kasuwar ba; tun da sun sayo da tsada ya zama dole su ma su lafta kudi”, a cewar tasa.
Sai dai ya ce, shanu dai kam su ne ke da matukar tsada a bana; inda ya ce farashinsu ya fara ne daga Naira 350,000, 400,000, 500,000 har zuwa 1,000,000.