Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da batun da muke yawan tattaunawa a kai cikin wannan shafi, wanda ya shafi kazanta, duba da yadda wasu mutanen ke samun kalubale game da kazantar mazajensu ko matayensu ko kuma samari da ‘yan mata, tare da yawan sakonnin da wannan shafi ke cin karo da su na son kara tattaunawa a kan wannan matsala.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin Taskira game da wannan batu; Ko tsakanin Mata da Maza wa ya fi wani Kazanta? Kawo Dalilai ko Hujjoji game da hakan, ko wacce kazanta ce ta fi kowacce kazanta game da mace da kuma namiji?, Shin an taba cin karo da kazama ko kazamin da ba a taba ganin irin kazantarsa/ta ba? Idan me kazanta na son komawa me tsafta wane mataki zai bi domin canja rayuwarsa zuwa tsaftaceccen mutum?
Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Zainab Alhassan Hassan, Gusau Jihar Zamfara:
Tab! di jan, magana ta domin Allah Mata sun fi kazanta bataccan ma kazanta, saboda namiji duk yadda zai yi yayi kazanta kanshi kawai zai wa kazanta ma’ana; Jikinsa, suturatsa, da sauran abubuwan amfaninshi na jiki. Amma mace kin ga za ta yi kazantar daki, gida, kwanonin wanke-wanke hatta da abincin da za ta dafa ma a kazance za ta dafa shi, kazantar jikinta, ‘ya’yanta idan tanada su to, kin ga mace tanada gurare da yawa wadanda za ta yi kazanta da su, hatta bandakinta indai kazama ce ba za ka iya hadiyar yau cikinshi ba. Gaskiya kazantar da ta fi kowacce kazanta a game da mace ko namiji ita ce; kazantar jiki, dan wannan kazantar ta fi kowacce kazanta daga hankali, saboda idan aka ce maka mijinka kazami ne to, hatta da bakinshi ma baka son ka matso kusa da shi, da yayi magana bakya iya shakarta, dan bakinshi warin da zai yi ya isa, sannan ita ma mace haka nan idan ta zama kazanta ta ci to, duk sauran kazantar sunada sauki bisa kazantar jiki. Ki ga ta shiga cikin mata ‘yan’uwanta tana wari, warin hammata, warin baki, warin ita kanta suturar, ga ta tayi dama-dama da kaya to, kazantar kai duk ta fi kowacce kazanta. Gaskiya ban taba haduwa da kazantar da ta kai irin kazantar dana ci karo da ita ba, saboda a kwai wata mata kazantar ta baci Awara take siyarwa, yara ne za su siyo Awarar amma karshe dan albasar da za a zuba musu da dan kayan miyan da take yankawa a cikin Awarar to, sai a iya samun kyankyaso a ciki, za ki ga albasa hade da mataccen kyankyaso ciki. Sannan ita kanta Awarar ma da a ka soya wari take yi saboda ba a samu tsafta gurin yinta ba, sannan idan ka shiga gidanta tun daga farkon shiga za ka fahimci gidan kazamai ne. Wanke-wanke kuda na bi, can tukwane sun yi gajen-gajen, diyanta majina duk ta bushe dauda duk ta yi musu kambarora ga abun nan, gabadaya inda take kwana ni ko Akuyata ba zan bari ta kwanta a wurin nan ba, a nan kusa da ni take wannan karamar kazanta na fada miki, dan za ki iya isko kashi cikin wanke-wanke fo din kashi tab da kashin yara, kuma ga shi ga kayan wanke-wanke kuda na bin kashi kuma suna bin kayan wanke-wanke.
Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya a kowane bangaren na maza da mata akwai kazamai, kuma akwai masu tsafta to, amma magana ta gaskiya an fi samun kazamai da yawa a bangaren mata domin su jikin a rufe yake kodayaushe, don haka sai sun ga dama suke tsaftaccewa, a lokuta da dama basu damu da kula da wasu sassan jikin nasu ba. To dalili a nan shi ne; su suna rufe jikinsu, wannan dalili ne ya sa da yawansu ba sa damuwa wajen kula da jikin, domin suna ganin da zarar sun yi lillibi shikkenan babu wani wanda zai gane sun yi tsafta ko basu yi ba. To a bangaren mata dai magana ta gaskiya mafi yawansu ba sa son wankewa da gyara kansu, domin mata da yawa suna da wannan matsala. To bangaren maza kuma an fi samun wadanda ba sa son wanke bakinsu da kuma wankewa riguna ‘Yan ciki ma’ana (Under wear) wannan na daya daga cikin matsalolin rashin tsaftar da maza ke sakaci wajen kula. To magana ta gaskiya na sha haduwa da maza masu irin wannan matsala ta rashin tsafta ko sakaci wajen kula jiki musamman a wajen taron jama’a a lokuta da dama ana haduwa da irin wannan matsala. To mataki na farko dai ya kamata ya sa a ransa tsafta wajibi ce domin wani yanki ne na Imani da addini kansa baya karbuwa sai da ita, na biyu muddun kana so al’umma suna mu’amula da kai dole ne ka dauki dabi’ar tsafta a matsayin abu mai muhimmanci a rayuwarka kodayaushe kana jin abun a ranka domin kada ka maimaita sakacin da kayi a baya.
Sunana Ayshatu D Sulaeman Daga Jihar Gombe:
Ni dai a nawa ganin matane suka fi kazanta, dalilina shi ne; musanman lokacin sanyi za ki ga mace bususu kafa duk faso, jiki duk tsami, sannan daki duk zarni, jikin yara duk datti kadan kenan daga ciki. Kazantar da ta fi kowace a wajen mace shi ne; Kazantar jiki sai wajen girki, sannan daki. Maza kuma namiji ya bar jikinsa yana wari irin samammin nan, ka ji suna wari kamar baragurbin kwai, ya kamata a kiyaye. Na taba ganin kazanta lokacin da na je wani gida ba ji ba shiri nayi saurin barin gidan, lokacin damina ne daman gidan ana kiwon awaki da sauran dabbobi, an yi ruwa wajen ya jagale da kashin awaki ga zarnin bandaki ba wankewa, ga tsamin kayan datti, na ga wannan zahiri. Muddin kana son komawa mai tsafta matakin farko shi ne; ka cire ganda a al’amarinka dan tana jaho kazanta, sannan sai ana yin wanka, wanki, shara, gyaran gida, gyara yara, da duk abin da ya shafi wannan gidan to, in sha Allah za a zama me tsafta.
Sunana Sulaiman Kabiru Bununu A Jihar Bauchi:
To magana ta gaskiya Mata sun fi kazanta a kan maza, su Mata wasu mutane ne da abu kadan kan nuna kazantarsu kamar wanka da wanki wani sa’in da ka ga mace ta fuskarta kamar tana tsafta amma abun daga ciki yake, mace za ta iya kwana biyu zuwa uku ba tayi wanka ba, Amma za ka ganta a fuskarta kamar ta yi wanka, namiji kuma kwaskwarima ma ya bukatar mashi. Kazantar da tafi kowace kazanta ita ce rashin wanka. Eh na taba gani, misali kamar; macen da na taba gani ita ce wadda take saka kaya a jiki ta dauki datti da kuma duk aikin da tayi ba za ta taba canzawa ba. Eh tabbas akwai, yanada kyau ya bi mataki-mataki da kuma zama da wadanda suke da tsafta saboda a zama ne da su kan iya sa mutum shi ma ya koya.
Sunana Fatima Tanimu Ingawa Jihar Katsina:
A ganina maza sun fi mata kazanta, dalili kuwa shi ne sun fi mata hidindimu da zirga-zirga sosai ta yadda suke tara zufa sosai dana wahalhalu, wanda in ba a samu masu kula sosai ba nan-da-nan sai jiki ya sauya yanayi zuwa ga abun da hanci bai so. Wannan ya sa maza ake son su rika ta’ammali da turaruka masu karfi, kama daga mai maiko zuwa na fesawa, wanda su kan sa bayan sun gama tsaftace jikinsu ba tare da barin wata dauda ko wata kazantar ba. A yau din nan ma na shiga kasuwa, wallahi sai da na dauke numfashi na da wani ya gifta ni saboda tashin kari. Rashin tsaftace jiki da tufafi ke sanya da an dan samu jigatuwa kadan sai yanayin jiki ya sauya da zaran zufa ta soma ketowa. Wannan na faruwa ne ga jikin da bai samun wadattaciyar kulawa ta tsafta ba, wanda inda da kula zufar ba za ta zama mai cutarwa ba. Hanyar da za a magance wannan shi ne. A rika tsaftace jiki sosai kama daga aski da sauransu, sannan kananan tufafin dake jiki a rika sauya su akai-akai. Bayan nan kuma sai a nemi turaruka masu armashi a bi dasu. Allah ya sa duk a gane a gyara.
Sunana Muhammad Isah Zareku Miga, Jihar Jigawa:
Na farko dai ni a nawa bangaren mata sun fi kazanta, saboda za ka je gidan matar aure ka ga gida ba shara, ga kayan wanke-wanke, ga kayan wanki ko kaya a mawanka a tare duk a guri daya babu wanki, ka shiga ka ga mace futu-futu da ita musamman a kauye da daurin kirji. Dalilin kuwa shi ne; yawanci wasu kazantar ta samo asali ne daga gida saboda ‘ya’yan masu hali ne sun taso da ‘yan aiki a gidansu to idan kuma a ka aurensu sai su kasa wannan dawainiyar sai su kasa, wani dalilin kuma saboda karancin gata basu da hali wajen sa ‘yan kilin ko omon wanke-waken ko tana son wanki ba samu za ta yi ba. Kazantar da tafi ita ce; rashin wanka a kai – a kai, za ka ga mutum har kuraje ya ke yi ko kwarkwashi saboda rashin samun wanka lokaci zuwa lokaci. A wani lokaci na taba ganin wata mace a asibiti dukka jikinta, yaron data kawo, kayan jikinta, hatta katin asibiti ba shi da kyan gani saboda kazanta kuma a haka kili lin taka wo wato irin ruga kafin nan da ake yi wa yara. Idan mai kazanta yana so ya dawo mai tsafta na farko ya gyara jikinsa, saboda manzon Allah (S. A. W) yana cewa; “Annahzafatu minal imani” ma’ana tsafta tana cikin cikon imani.
Sunana Hadiza Muhammad, daga garin Gusau Jihar Zamfara:
A gaskiya ni a ganina maza sun fi kazanta, dalilaina su ne kamar haka;Â In kina da yara maza da mata, za ki ga mazan sai kin yi da kyar ki samu yayi wanka, amma mace ba za ma ki yi mata magana ba za ta yi. Maza duk inda suka samu sai sun zubar da kayansu, sabanin mace, ita sai ta kimtsa. In ki ka shiga dakin wasu samarin miyau ma sai ya miki wahalar hadiyewa. Kazantar da tafi kowace kazanta a wurin mace ita ce; rashin kula da kai lokacin al’ada. Namiji kuma, yawanci ba sa flushing in sun yi bayan gari. Na taba gani, wata mata ce duk lokacin da take al’ada ba za ta wanke kyallen da take amfani da shi ba, ko dan kamfanta, sai tayi ta tara su har sai ta gama. Hanya daya ce, ya tuna cewa tsafta tana daga cikin imani, da zarar ka sa wannan a ranka to za ka bar kazanta ka rungumi tsafta.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Daga Jihar Kano Rano:
Mata sun fi maza ba wai domin ina namiji ba. Dalili na kuwa shi ne; mata sune girke-girke da shara da sauransu. Hujjata kuwa ita ce wasu matan wallahi idan suna aiki gani suke yi a cikin gida ne babu wanda zai gansu koda abincin siyarwa ne wani ma idan ka gani ba za ka sake sha’awar irin wannan abincin ba. Rashin wanka da wanki, sannan wasu matan sharar gida ma basa son yinta ko ka ga kwanukan cin abinci kaca-kaca babu wanki. Eh ni dai bana son na ji mace mai irin warin kashi wanda mafiya yawan mutane da haka suke cewa amma ni gani nake wasu rashin tsafta ne yake saka wannan warin koda mutum yayi wanka ya saka turare idan ku ka hadu sai ka ji wannan warin wanda maza da mata ana samun irin wannan. Shawarar da zan bawa kazami ko kazama domin dawowa mai tsafta ita ce; Mutum ya tuna ita kanta ma tsaftar tana daga cikin addininmu na islama, sannan koda a rayuwarka/ki sai kun fi jin dadin rayuwar balle ku shiga cikin Al’umma har wani ji da kai za ka ji kana yi. Allah ya sa mu dace.
Sunana Hassana Sulaiman Hadejia A Jihar Jigawa:
Uhmmmm babbar magana wai aka ce dan sanda ya ga gawar soja , yau maudu’in kusan haka ya fuskanta. Kusan maganar gaskiya a nan kowane bangaren za a iya bashi kaso 50/50 sai dai wasu bangaren na mazan zai iya daukar kaso 70% cikin 100% , idan aka saka kan sikeli zan iya cewa mazan su suka fi kazanta ku yi min afwa iyayena maza. Dalina da hujjoji na a kan hakan kuwa shi ne; dauki iya faso kadai da wasu daga cikin mazan ke bari a kafarsu, rashin kulawa da tsaftar bakinsu ,rashin kulawa da tsaftace jikinsu wajan barin duk wani abun da zai fitar da wari a tare da su wanda hakan na cutar da mata Æ™warai da gaske. Kazantar da tafi kowace kazanta tsakanin kowane bangaren na mazan da matan ni dai a nawa mahangar bata wuce ta rashin sanin kai ba, ma’ana kai matsayinka na mutum baka san hanyar da za ka sarrafa tsaftar jikinka ba, da kuma wanda za kuna fitar da wani nau’in wari a tare da kai/ke wannan kamar ita ce kazantar da tafi. Tabbas indai kana duniya za ka ce ka taba ganin mace kazama da kuma namiji shi ma kazamin! Misalin hakan kuwa; wasu daga cikin matan idan ka shiga cikin gidan su koda ruwa ba za ka iya sha ba na ga wannan kuma na ci karo da hakan da dama. Kusan idan mutum na so ya dawo mai tsafta daga marar tsafta abu ne mai sauki sosai komawa hakan, na farko ka lazimci kusantar masu tsafta kuma ka sanya a ranka cewa kai ma/ke ma z aka/zaki iya zama kamar shi da ya ke burg eki/burge ka, sannan ka fara gwada daina wasu abubuwan da ana ganinsu za a iya fassara ka da cewa wane kazami/wance kazama ce, sannan dadi da kari kuma uwa uba dole sai an cire kiwa da ganda za a samu gyaran idan ba a cire wadanna ba gyaruwar daga kazami zuwa mai tsafta zai yi wuya gaskiya.
Sunana Hafsat Sa’eed Daga Jihar Neja:
Gaskiya abin da ni na fi hange shi ne; maza sun fi mata kazanta, dalilina kuwa shi ne; Mace duk kazantarta tana gida dai za ta iya gyara waje, za ta gyara ‘Ya’ya, duk tana kazantar dai dole ba za ta bar ‘ya’ya da datti ba, za ta shirya yara su je makaranta, da tsaftar daki za ta iya barin daki da kaya baje-baje, indai ba wai ta shahara a kazanta bane, duk da cewa a kwai matan da kazantarsu ba a cewa komai, amma dai maza sun fi mata kazanta sosai. Yadda kazami zai koma mai tsafta abu ne me sauki, matakin da zai fara da shi idan namiji ne ya kasance yana wanka yana gyara jikinsa dole ya tirsasawa kansa hakan kuma ya rika fesa turare. Haka idan mace ce ta rika gyara muhallinta wajen zama tana tashi ta fada wanka a kullum kar ta bari hakan ya wuce ta, da yamma ta kara samu ta shiga wanka a kalla dai ko sau biyu ne ta rika wanka kullum tana saka turare tare da tsaftacce duk guraren da suka kamata.
Sunana Usman Adamu Malam-maduri A Jihar Jigawa:
Duba da yau da kullum da muke da mata kuma da maza, mata sun fi maza kazanta, dalilina ko hujjojina na fadar hakan shi ne; mata suna nuna kazantarsu ne a gurare daban-daban, musanman a cikin gida domin a cikin gida mace ta kan yi yawo a cikin gida babu takalmi a kafarta, kuma ta shiga duk inda take so ta shiga ba tare da hankalinta ya tashi ba, ko kuma ta fito farfajiyar gida babu dankwali a kanta a kan samu akasi ma wani lokacin kan babu kitso gashi ya kan iya tashi ya je duk inda ya ke so ya je ba tare da ta gane wannan abun kazanta bane, wani lokacin idan kasa ido za ka ga kafin mace tayi wanka sau daya tayi kwaskwarima sau biyar, wannan ma babbar kazanta ce, balle uwa’uba gurin kwanciya wannan ba a magana. Kazantar da tafi kowacce kazanta a tattare da mace ita ce; rashin yin wanka akai- akai da gyaran hakori, shi kuma namiji rashin yin aski kuma ba za a gyara gashin ba da kuma rashin yanke farce akai-akai. Eh! kwarai kuwa hakan yana yuwa domin wanin ko watan ba za ka taba ganin kazantarta ba ko kazantarsa ba sai an zama daya, domin kafin a zama dayan kowanne tsaf-tsaf za ka ganshi. Duba da bincike na da tunanina babu abin da ya ke sa me kazanta ya koma mai tsafta musanman ga ‘ya’ya mata shi ne; a ce sun fara kaiwa wani (age) da namiji zai ganta ya ce yana sonta ita kuma burinta ta fito tsaf-tsaf ya ganta shi ne burinta to, wannan zai sa duk kazantarta ta koma mai tsafta.
Sunana Aisha T. Bello, Daga Jihar Kaduna:
Maza sun fi kazanta, saboda da yawansu za ki ga sun yi wanka an sa turare amma dakin duk datti babu gyara, wasu dakin na wari amma za su sa turare su fita, tsaf-saf kamar basu bane ke kwana a kazamin muhalli. Yawancin maza fa sai sun yi aure suke fara tsafta, dalili kuwa maza da yawa na kafa hujja ne da aikin gida na mata ne, wasu mazan ma hatta shara da gyaran muhalli suna dauka cewa na iya mata ne ba na maza ba, da yawansu suna kafa hujja ne da wannan su tsula kazantar su a bayan fage. Amma duk da hakan ban ce duka ba, don a wani bangaren akwai maza masu tsafta wanda sun fi wasu matan ma. Shawarar da zan bayar ga irin mazan dake ganin gyaran muhalli na mata ne kadai shi ne; ya kamata su farka su san tsafta fa ba a kan iya mata ya wajabta ba, hadda su ma mazan. Don kuwa akwai kananun cututtukan da kan iya kama mutum ta dalilin rashin tsafta, kun ga a nan sai mu ce waye gari ya waya? Allah ya sa mu dace