Connect with us

RA'AYI

Tsakanin Minista Akpabio Da Masu Yi Masa Yarfe Da Cin Mutunci

Published

on

Marigayi Mahatma Ghandi ya taba cewa kafafen watsa labarai manyan turaku ne wurin kawo sauyi. Sai dai ya yi gargadin cewa idan aka tafiyar da kafafen ba ta hanyar da ta dace ba, maimakon su kawo sauyi na ci gaba, sai su haifar da Baraka. Don haka kafafen watsa labarai kamar takobi ne mai kaifi biyu, za a iya aikata barna da shi, ko a aikata alheri.

A daidai lokacin da mutanen kwarai suke amfani da kafafen watsa labarai wurin aikata alheri da neman kawo ci gaba, su kuma mutanen banza suna amfani da kafafen sadarwan ne wurin haifar da rikici da cin zarafin mutane.

Wadannan misalai na sama suna bayyana inda masu yi wa Akpabio yarfe suka fada. Saboda ganin yadda tsohon gwamnan na Akwa Ibom kuma tsohon sanata, sannan a yanzu ministan ma’aikatar Neja Delta yake samu ne ya sa ‘yan yarfe da cin mutunci suka sako shi gaba da cin mutunci da yada karairayi domin kawai su dauke hankalinsa daga aikin da ya sa a gaba.

Wadannan ‘yan yarfen sun yi amfani da wata mujallar da ba a ma santa ba a bugunta na wannan watan na Yuli inda suka wallafa karairayi da shirme da sunan su bata sunan Minista Akpabio.

Daga binciken da na yi, wanda har ta kai na je Neja Delta domin tattaro bayanai, zan iya bugun kirji a ko ina ne na ce wannan rahoton na mujallar babu komi a cikinsa face karairayi da kirkirarrun labarai. A gabadaya rahoton an ci zarafin ka’idojin aikin jarida, sannan marubucin ya yi amfani da son ransa wurin yin aikin cin mutuncin da aka biya shi kudi ya yi.

Dabi’a mai kyau ita ce muhimmiyar aba a rayuwar dan adam. Duk wanda bai da dabi’a mai kyau za ka gansa sai a hankali. Ministan Ma’aikatar Neja Delta, Obong Godswill Akpabio ya yarda da kiyaye dabi’arsa ta kirki, shi ya sa a duk inda ya tsinci kansa yake son yin komi bisa tsari da nuna kamata.

Shi Akpabio ya san wanne aiki ke gabanshi, sannan kuma ya san dalilin da ya sa Shugaban Kasa Muhammdu Buhari ya ba shi shugabancin Ma’aikatar Harkokin Neja Delta. Akpabio ya kwana da sanin cewa ba zai watsawa Shugaban Kasa Buhari kasa a ido ba. Haka kuma Akpabio yana sane da irin rashawa da rashin gaskiyan da aka tafka a Ma’aikatar Kula da Harkokin Neja Delta.

Domin tsaftace barnar da aka aikata, da zuwansa Akpabio ya nemi da a bashi rahoton duk wani kudi da aka kashe. Wannan matakin da ya dauka ne ya matukar harzuka masu bibiyan ministan da yarfe, domin a baya sun mayar da ma’aikatar wata saniyar tatsa, babu ruwansu da kishin yankin.

A kokarinsu na bata mishi suna, sun yi ta yada cewa Akpabio ya bayar da aikin ruwa wanda sam ba a yi aikin ba. Wannan karya ce tsagoronta. Ai kowa ya sani cewa kafin a yi wa Akpabio minista, babu wani aikin raya kasa da ke tafiya a yankin Neja Delta. Amma ku kalli irin karyar da suke yadawa babu kunya ba tsoron Allah.

Wai wanne Sanata suke magana ne akai? Akpabio din da ya sauyawa Jihar Akwa Ibom fasali zuwa cigababbiya har ta zarce tsara? Idan har a tarihinsa ba a taba kama shi da laifin sata ba lokacin yana gwamna, me zai sa ya yi sata bayan ya zama minista?

Ko ma mene ne manufar wadannan mutanen, sun yi a banza. Domin babu wanda zai yarda da wadannan karairayin nasu. Yadda lamurra suka nuna, mahassada da makiya sun fito kwansu da kwarkwata da zimmar batanci ga Akpabio. Sun yi irin wannan kamfen din don su ga ba a yi mishi minista ba, amma hakan bai yiwu ba, har yanzu kuma ba su saduda ba.

Sun sha alwashin cewa ba za su hakura da kokarin yin batanci ga Minista Akpabio ba. Shi ya sa ma yanzu suke bi ta kowacce hanya da suke ganin suna da ita na yin yarfe gare shi.

Wannan cin mutunci da yarfe da wasu suka dauki nauyi, kana gani ka san cin hanci da rashawa ne ke kokarin mayar da martani daga ragargazarsa da ake yi a ma’aikatar harkokin Neja Delta. Duk fa matsalar tana cikin matakin da Akpabio ya dauka ne na cewa a ba shi rahoton kudaden da aka kashe a baya. ‘Yan rashawar da ake tuhuma kuma aka dakile wa hanyoyin sata ne suke daukar nauyin wannan yarfe da cin mutunci.

Duk fa abin da mutanen ke yi ya fi kama da kokarin ba kare sunan banza domin a rataye shi. Idan da gaske Akpabio ya yi satan da suke fadi a Akwa Ibom to ta ya kuma ya iya yin ayyukan da ake iya gani yanzu a kasa a jihar?

Marubucin ya yi zargin cewa Sanata Akpabio yana amsan kso 10 zuwa 15 daga yankuna a Neja Delta kafin a aminta a sa hannu kan aikinsu. Wannan zancen ma da ji an san karya ce.

A rahoton da mujallar karyar ta wallafa ta yi ikirarin cewa Akpabio ya kauracewa majalisar zartaswar tarayya inda ya koma Fatakwal da zama. Wannan ma zancen banza ne daga mutanen banza. Ko kadan babu kamshin gaskiya a maganar tasu.

Duk dan Nijeriya na gari bai kamata ya yarda da wadannan karairayi da aka kirkira kan Akpabio ba, domin mutum ne da ya yi tsayuwar daka wurin ganin ya tsaftace Cibiyar NNDC. Wannan ba komi ba ne face farfaganda irin ta masu yarfe, wadanda ke son daukewa ministan hankali daga muhimman ayyukan da ke gabansa.

  • Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da Tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa ‘Presidential Support Committee’ (PSC)Advertisement

labarai