Daga Muhammad Maitela,
Bisa zargin tsarewa ba bisa ka’ida ba ya jawo an maka shugaban sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, babban kwamandan rundunar sojojin yanki ta bakwai (General Officer Commanding 7 Division) tare da babban Antoni na kasa kuma minista a ma’aikatar shari’a ta Nijeriya, zuwa babbar kotun Nijeriya (Federal High Court) da ke Maiduguri bisa tsarewa ba bisa ka’ida ba.
Takardar karar mai dauke da lamba FHC/MU/CS/1/2021 wadda Alhaji
Ibrahim Shehu Damakosu da Sabo Yahaya su ka shiga a gaban kotun tare da gabatar da bukata ga kotun ta bi musu hakkin su na dan Adam kamar yadda sashe na 46 (3) ya nuna a kundin tsarin mulki na 1999 ya nuna; wanda aka yi wa gyaran fuska.
Saboda haka sun bukaci kotun ta tilasta wa wadanda suke karar su gabatar da su gaban kotun da ta dace domin tuhuma nan take daga tsarewar da ake musu ba bisa kan doka ba.
Bugu da kari kuma, sun nemi a biya su diyyar naira miliyan 100 tare da neman afuwarsu a rubuce da wani umurnin kotu saboda nan gaba idan bukatar hakan ta taso. Sannan ba a sanya lokacin sauraron karar ba.