Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na ganin cewa, wasu manya da kananan kamfanoni sun amfana da dala biliyan 50 da aka ware, domin gudanar da tsarin ‘yancin kasuwanci a yankunan Afirka ba tare da fuskantar matsala ba.
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya bayyana haka, a ranar yayin kaddamar da shirin kula da harkokin kasuwanci da aka samar karkashin yankunan kasashen Nahiyar Afirka.
Haka zalika, Shugaban ya bayar da tabbacin cewa; gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa kamfanonin Nijeriya a kowane mataki, domin tabbatar da ganin sun ci gajiyar wannan shiri na kasuwancin yankunan kasashen Afirka. “Za a mayar da hankali wajen bin muhimman abubuwan da ke da muhimmanci tare da tabbatar cewa, dukkannin wani kamfani na Nijeriya, tun daga kan kanana da matsakaitan masana’antu har zuwa manyan kamfanoni, za su ci gajiyar wannan yarjejeniya. Saboda haka, gwamnati za ta ci gaba da bayar da tallafin da ya dace, domin saukaka aiwatar da shirin yadda ya kamata, a matkin gida, yanki da kuma nahiyoyi,” in ji shi.
- Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Sin Da Turai Da Su Aiwatar Da Takara Mai Tsafta Don Cimma Nasara Tare
- Zamfara Za Ta Bunƙasa Ta Dawo Matsayinta Na Dandalin Kasuwanci A Arewa – Gwamna Dauda
Sannan, ya yi kira da a hada karfi da karfe, domin samun nasarar wannan shiri, yana mai kuma sake jaddada aniyar gwamnatinsa na yin aiki tukuru, domin cimma wannan buri.
“Bari mu sake tabbatar da aniyarmu ta yin nasara a kan wannan shiri na kasuwancin yankunan nahiyar Afirka, ta hanyar yin aiki tare da kuma himma, don cimma ma’ana daya a yayin da muka fara wannan tafiya. Don haka, gwamnatina za ta yi aiki tukuru don ganin kowane dan Nijeriya ya ci gajiyar wannan yarjejeniya mai matukar dimbin tarihi. Har ila yau, bari in kara da cewa; za a karfafa tsarin hukumomi da na doka, don taimakawa wajen cimma wadannan manufofi,” in ji shi.
Haka zalika, sakamakon kaddamar da wannan shiri na kasuwanci, Tinubu ya bayyana wani gagarumin ci gaba da aka samu, inda ya zayyana shi a matsayin wani abu wanda zai haifar da harkokin kasuwanci tsakanin kasashen Afirka tare kuma habaka tattalin arziki da kuma ci gaba mai dorewa.
Tinubu ya kara da cewa, dandalin zai bude sabbin kasuwanni ga kayayyaki ko hajojin Nijeriya tare da kara samar da gasa da kuma ayyukan yi.
Ko’odinata na kungiyar ta kasa, Mista Olusegun Awolowo; ya jaddada cewa, jarjejeniyar na da matukar amfani musamman ga dimbin albarkatun Afirka wajen sanya masana’antu da al’ummar matasa cikin tsarin tare kuma da saukaka ci gaban tattalin arziki.
Har ila yau, Awolowo ya jaddada cewa, kasuwanci ne hanya mafi dorewa wajen samun wadata, sannan ya bukaci Nijeriya da sauran kasashen Afirka da su yi kokarin samar da hanyoyin fita daga cikin kangin talauci, rashin aikin yi da kuma tabarbarewar matsalar tattalin arziki.
“A yau, bayan cika dukkanin sharadodin yarjejeniya da aka tsara don, tabbatar da wannan shiri na kasuwanci; mun tsaya a matsayinmu na shaida kan yadda za a aiwatar da wannan kasuwanci a hukumance, a karkashin wannan tsari na ciniki na musamman tare da jigilar kaya daga tashar jiragen ruwa na Apapa,” in ji Awolowo.
Haka nan, Awolowon ya bayyana cewa; bayan kaddamar da aikin a hukumance, kamfanoni goma ne za su fara fitar da kayayyakin Nijeriya zuwa kasashen biyar gabashi, tsakiya da kuma Arewacin Afirka.
“Wasu daga cikin kamfanonin sun hada da kamfanin ‘Le Look Nigeria Limited’, wanda zai fitar da jakunkunan zuwa Kasar Kenya tare da wakiltar dukkanin ‘yan kasuwa mata, sai kamfanin ‘Secure ID Limited’, wanda zai fitar katin na musamman zuwa Kasar Kamaru, sai kuma kamfanin Dangote shi ma da zai fitar da kayan zuwa Kasar ta Kamaru,” kamar yadda ya bayyana.
Ministar Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Doris Uzoka-Anite, ta nanata kudirin Nijeriya na ci gaba da kuma gagarumin alkawarin da yankunan kasashen Afirkan suka yi na bunkasa ci gaban masana’antu.
Sannan, ta yi kira ga masu ruwa da tsaki das u hada karfi da karfe wajen tabbatar da samar da ayyukan yi ga jama’a, tare kuma da yin amfani da dandalin wajen amfani da damammakin da ake da su.