Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) ta bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara da ya umurci Ministan Ma’adanai da ya dakatar da haƙar ma’adinai na tsawon watanni shida domin a ba da damar gudanar da ƙwaƙƙwaran bincike.
Ƙungiyar ta ce ta lura cewa, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba na zama babban abin da ke haifar da matsalolin tsaro a Arewacin Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya karanta, bayan taron haɗin gwiwa na Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa da aka gudanar a Kaduna ranar Litinin, ƙungiyar ta ce ta kafa Asusun tallafin Tsaro na Yankin inda kowace jiha za ta riƙa bayar da gudunmuwar Naira biliyan 1 duk wata-wata a ƙarƙashin tsarin da za a amince da shi.
A cewar sanarwar, “Taron yana mika ta’aziyya da goyon baya ga Gwamnatoci da mutanen kirki na jihohin Kebbi, Kwara, Kogi, Neja, Sokoto, Jigawa da Kano bayan kisan gilla da sace yaran makaranta da sauran ‘yan ƙasa wanda ba su ji ba su gani ba, da kuma waɗanda hare-haren Boko Haram suka shafa a jihohin Borno da Yobe.
“Taron yana yaba wa Gwamnatin Tarayya, karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, saboda jajircewa wajen tabbatar da sakin wasu daga cikin yaran da aka sace cikin gaggawa da kuma magance wasu kalubalen tsaro. Haka kuma muna yaba wa sadaukarwar da sojojinmu suka yi wadanda ke ci gaba da yaki da nau’ikan tashe-tashen hankula daban-daban a fadin kasar.
“Taron ya sake jaddada goyon bayansa da jajircewarsa ga kafa ‘Yansandan Jiha. Saboda haka, taron yana karfafa wa ‘yan majalisar dokoki na kasa da na jihohi a yankin da su hanzarta daukar mataki don aiwatar da wannan kudiri,” in ji sanarwar.














